1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokokin Libiya

June 25, 2014

'Yan ƙasar Libiya na gudanar da zaɓen 'yan majalisa ƙarƙashin yanayi na rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta

https://p.dw.com/p/1CPgH
Hoto: Reuters

A wannan Laraba 'yan ƙasar Libiya ke gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokoki. Yayin zaɓen za a zabi 'yan majalisa 200 da za su maye gurbin majalisar dokoki ta wucin gadi da aka zaɓa a shekara ta 2012. An ware wa mata kujeru 32 daga ciki.

Ana fatan zaben zai kawo ƙarshen taƙaddamar siyasa da zaman tankiya da ƙasar ta samu kanta a ciki, shekaru uku bayan juyin-juya halin da ya kawo ƙarshen gwamnatin Marigayi Mu'ammmar Gaddafi. Ƙasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka tana cikin ƙasashen duniya masu arzikin man fetur.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane