1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kan neman Jirgin EgyptAir da ya bace

Zainab Mohammed AbubakarMay 19, 2016

Ma'aikatar harkokin sufurin sama ta Masar ta sanar da cewar, da sauran lokaci na sanin halin da jirgin sama kirar Airbus A320 mallakar kamfanin EgyptAir da ya bace ke ciki.

https://p.dw.com/p/1IqIp
Egypt Air Kairo Flughafen
Hoto: picture-alliance/dpa/K.Elfiqi

Sakamakon binciken da aka gudanar tun da farko ya nunar da cewar, jirgin wanda ke dauke da mutane 66 a cikinsa bai sauka a kow ne filin jirgi da ke kasar ta Masar ba.

Jirgin ya bace ne bayan shigarsa sararin samaniyan Masar da wajen km 16, mintuna 20 kafin ya sauka da misalin karfe uku da miniti biyar na safiyar wannan Alhamis.

Fasinjoji 56 da ma'aikatan cikin jirgi shida da kuma jami'an tsaro guda uku ne ke cikin jirgin da ya baro Paris cikin daren jiya da nufin sauka a birnin Alkahira da safiyar wannan Alhamis.

Mutanen cikin jirgin sun kunshi 'yan Masar 30 da Faransa 15, a yayin da sauran suka fito daga kasashe daban daban 10

Tuni ministan sufurin sama na Masar Sharif Fathy ya yanke ziyarar aiki da yake yi a kasar birnin Jeddah na kasar Saudi Arabiyya.