1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kidaya kuri'a cikin tsaro a Bangui

Kamaluddeen Sani ShawaiDecember 31, 2015

Kuri'un da aka kidaya a zaben Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya ba su taka kara sun karya ba. Amma kuma an tsaurara matakan tsaro a cibiyar hukumar zabe da ke Bangui.

https://p.dw.com/p/1HWdq
Afrika Wahlen in Zentralafrika
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tabbatar da tsaro a cibiyar kidaya kuri'u a Bangui na Jamhuriyar Afrika Ta tsakiya a daidai lokacin da hukumar zaben kasar ta fara kidaya kuri'un zaben da aka gudanar.

'yan kasar sun futo kwansu da kwarkwata a ranar Laraba don zaban shugaban kasa da mambobin majalisar dokokin kasar ba tare da wani hayaniya ba, abin da shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniyar Onnga Anyanga ya jinjina da cewar zaben ya sami nasara.

An dai dauki kwararan matakan tsaro ne bisa kaucewar barkewar yamutsi da ka iya barkewa bayan kammala zabe kasar. Mai yiwuwa ne dai hukumar zaben ta bayyana sakamakon zaben nan da wasu kwanaki kalilan masu zuwa.