1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana nuna alhini game da harin bom na Abuja

June 26, 2014

'Yan uwan mutanen da suka samu raunuka a harin Abuja na ci gaba da tururuwa a asibitocin birnin, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta ce ayyukan ta’adanci ba su da wurin zama a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1CQa2
Hoto: Reuters

Yanayi na ban tausayi da tashin hankali ne ke marhabin ga duk wanda ya ziyarci asibitocin da aka kwantar da mutanen da suka jikata a sakamakon wannan mumunan harin bom da ya kashe mutane 22 a Abuja. Madam Uche Ojeh na daga cikin wadanda suke cikin damuwa tare da rusa kuka a asibitin unguwar Maitama, saboda ba ta ga mai-gidanta ba.. Ta ce " ya na tsaye a kusa da motarsa kafin bom din ya tashi. Amma mun duba ko ina har asibitoci babu labarinsa''.

Wasu daga cikin mutanen da suka samu rauni na kwance ne a asibitin Maitama. Daa daga cikinsu ya bayyana wa DW cewa " karfe ne ya sameni ,ya fasamin wando sanna nya huda fatar jikina ya shiga , don haka da aka yi min aiki sun duba sun fitar da karfe guda biyu''.

Tuni dai mataimakin shugaban Najeriya Namadi Sambo ya ziyarci wajen da bom din ya tashi inda ya bayyana cewa ayyukan ta'addanci fa ba su da wuri a Najeriya. Jami'an gwamnatin kasar na ci gaba da kai ziyara zuwa wurin domin nuna alhini da wannan mumunan hari . Hajiya Zainab Maina ita ce ministar kula da harkokin mata ta Najeriyar da ta bayyana cewa " Abin tausayi ne abin kuka ne wannan abin da ya faru."

Nigeria Vizepräsident Namadi Sambo
Namadi Sambo ya je ya duba wadanda suka samu rauniHoto: AFP/Getty Images

Wannan mumunan hari dai da yi kaca-kaca da ginin katafaren shagon na Emab Plaza ya sauya yanayin wannan titi da ma unguwar da ta kasance mai cike da cunkosun motoci da na jama'a. Sai dai jami'an tsaro na ci gaba da bincike, a yanayin da ya kara jefa tsoro da zaman zullumi ga mazauna birnin Abuja saboda yawaitar kai hare-hare na bom a birnin.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris daga Abuja
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe