1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana sukar Gambiya kan take hakkin dan Adam

Suleiman BabayoFebruary 18, 2015

Kasar Gambiya tana bikin cikin cika shekaru 50 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya

https://p.dw.com/p/1Edre
Yahya Jammeh 2006
Hoto: picture-alliance/AP/Rebecca Blackwell

Shugaban kasar ta Gambiya Yahya Jammeh wanda yakre mulkin kasar tun shekarar 1994 fiye da 20, ya bayyana kaddamar da bukuwa na tsawon watanni uku albarkacin cika shekaru 50 daga samun 'yanci daga Turawan mulki mallaka na Birtaniya.

Tuni kungoyoyin kare hakkin dan Adam suka soki yadda gwamnatin kasar ke ci gaba da daukan matakan take hakkin mutane musamman wadanda suke adawa da gwamnati.

Gambia Straßenszene in Banjul
Hoto: picture-alliance/maxppp/M. Aliou

Francois Patuel ya kasance mai bincike kan kasashen yammacin Afirka a kungiyar Amnesty International, wanda ya wanda ya nunar da yadda ake ci gaba da gallaza wa mutane musamman wadanda suke da sabani da gwamnati a bangaren siyasa.

Mustapha Khadi ya kasance na kungiyoyin kare hakkin dan Adam na hukumar kasashen Afirka wanda ya ce tun lokacin da Yahya Jammeh ya kwace madafun iko bayan juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin Dauda Jawara kasar ta fada cikin wannan yanayi.

A shekarar da ta gabata an yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar haka ya janyo kara daukan matakan babu sani babu sabo kan 'yan adawa.

USA-Afrika-Gipfel in Washington
Hoto: reuters

Ana zargin gwamnatin kasar ta Gambiya da cin zarafin fursunoni da saba matakan sharia, abin da Mustapha Khadi ya ce suna ci gaba da karar tsaye da dagula lamura, duk da cewa hukumar kula da kare hakkin dan Adam ta Afirka tana saka ido.