1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana taron dakile Boko Haram a Najeriya

Suleiman BabayoJune 11, 2015

A Najeriya shugabannin kasashe makwabta na gudanar da taro kan hadaka domin yaki da kungiyar Boko Haram

https://p.dw.com/p/1Ffnq
Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Sabon Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana karbar bakuncin shugabannin kasashe makwabta domin duba hanyoyin bai daya na yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram.

Shugaban dan shekaru 72 da haihuwa da ya dauki madafun ikon kasar makonni biyu da suka gabata, ya karbin bakuncin shugabanin kasashen Chadi, da Jamhuriyar Nijar, da Jamhuriyar Benin gami da ministan tsaron kasar Kameru, a taron na kwana guda da ke gudana a birnin Abuja fadar gwamnatin kasar.

Tashe-tashen hankulan kungiyar ta Boko Haram sun yi sanadiyar hallaka kimanin mutane 15,000 yayin da wasu fiye da milyan daya da rabi suka tsere daga gidajensu. Cikin watannin da suka gabata dakarun kasashen duniya sun gami da Najeriya sun kwato garuruwa da dama daga hannun 'yan Boko Haram. Shugaba Buhari ya shaida wa shugabannin kasashen cewa Najeriya za ta shiga gaba wajen yaki da Boko Haram. Tuni shugaban ya mayar da helkwatar rundinar yaki da Boko Haram zuwa Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno da ke zaman tungar kungiyar.