1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana taron koli kan tazarcen Nkurunziza

Mouhamadou Awal BalarabeMay 31, 2015

Kungiyar raya yankin gabashin Afirka na gudanar da taron koli a Tanzaniya kan rikicin siyasar Burundi musamman ma yunkurin tazarce na shugaba Pierre Nkurunziza.

https://p.dw.com/p/1FZbp
nach Putschversuch - Präsident Pierre Nkurunziza zurück im Amt
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka sun hallara a birnin Dar es salam na Tanzaniya da nufin gudanar da taron koli, wanda zai mayar da hankali kacokan da rikicin siyasa da ake fama da shi yanzu haka a kasar Burundi. Wannan kuwa ya zo ne a daidai lokacin da mataimakiyar shugaban hukumar zaben kasar ta Burundi ta gudu daga kasar tare da yin murabus, sakamakon adawa da al'umma ke ci gaba da nunawa game da yunkurin tazarcen shugaban kasa Pierre Nkurunziza.

Sama da wata guda ne dai kungiyoyin fararen hula da kuma 'yan adawan Burundi suka shafe, suna gudanar da zanga-zangar yin Allah wadarai da shirin Nkurunziza na neman wa'adin mulki na uku, lamarin da suka ce ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma a shekarun baya.

A cikin watan Yuni mai kamawa ne dai za a gudanar da zaben kananan hukumomi da kuma na 'yan majalisa, da ma dai na shugaban kasa da na sanatoti. Sai dai shugabannin kasashen yankin gabashin Afirka na nema shugaba Nkurunziza ya dage wadannan zabuka.