1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel za ta yi jawabi kan kyamar Yahudawa

Yusuf BalaSeptember 11, 2014

Jamus na ci gaba da bayyana adawarta ga shirin nuna kyama ga Yahudawa a duniya, wani abu da ke zama kokarin wanke kanta ga wasu abubuwa da ta yi a baya.

https://p.dw.com/p/1DAec
Deutschland IFA in Berlin Angela Markel
Hoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta yi jawabi a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus a ranar Lahadi kan taron gangami na nuna adawa da kyamar da ake nuna wa Yahudawa musamman ta kalaman batanci da ake nuna musu da ma farmaki wanda shi ne sanadin rura wutar rikici na baya bayan nan a Zirin Gaza.

Wannan taro kuwa na zuwa ne shekaru 75 da barkewar yakin duniya na biyu, wanda a lokacinsa Jamusawa masu akidar Nazi suka kashe Yahudawa miliyan shida, laifin da ya zamo wani abu da ake alakanta kasar da aikata wani abin kunya cikin tarihinta.

Taron da za a yi a gaban kofar nan mai tarihi ta Brandenburg a birnin Berlin zai dauki taken "A tashi tsaye: kyamar Yahudawa har abada". Zai kuma zo ne a daidai lokacin da za a gudanar da babban taron Yahudawa na WJC a fadar gwamnatin kasar.