1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel da Francois Hollande sun isa Moscow

Muntaqa AhiwaFebruary 6, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta Jamus da Francois Hollande na Faransa, sun isa Moscow don tattaunawa da shugaban Rasha a kokarin kawo karshen rikici a Ukraine.

https://p.dw.com/p/1EXUi
Merkel und Hollande zu Gesprächen mit Putin in Moskau
Hoto: picture-alliance/epa/S. Ilnitsky

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da shugaban Francois Hollande na Faransa, sun isa Moscow yau Juma'a don tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin dangane da kokarin kawo karshen zubar da jini a Ukraine.

Shugabannin biyu dai, kafin tashin su zuwa kasar Rashan, sun bayyana cewar ba lallai ba ne zaman na su ya kaiga samun nasara, ba kuma mamaki a sake wani zama dangane da wannan batu.

Shugaba Francois Hollande a nashi bangaren, ya ce matakin farko da zai kai ga maslaha, shi ne a sami tsagaita wuta daga bangarorin dake gaba da juna.

A jiya Alhamis ma Angela Merkel da shugaban na Faransa Hollande, sun gana da shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko a birnin Kiev, inda suka ce za su gabatar da shirin da zai dace da mutuncin Ukraine din.