1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta gana da fraministan Isra'ila

December 6, 2012

Benjamin Netanyahu ya fara tattaunawa da shugabar gwamnatin jamus a ziyarar da ya ke yi a birnin Berlin, a wani mataki na rangandin da ya soma a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/16wT3
Der israelische Ministerpräsident Benjamin Netanjahu und Bundeskanzlerin Angela Merkel unterhalten sich am Montag (31.01.2011) in Jerusalem (Israel) bei einem gemeinsamen Essen. Merkel und zahlreiche Minister sind am Montag (31.01.) zu den dritten deutsch-israelischen Regierungskonsultationen in Jerusalem zusammengekommen. Sie ist zu einem zweitägigen Besuch in dem Land. dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan ziyara ta Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ƙasashen na Turai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta ke shan suka daga ƙasashen duniya dangane da shrinta da ta cigaba da yi, na gina matsugunan Yahudawa a gaɓar yamma da kogin Jodan da kuma gabashin birnin Ƙudus.

Jamus wacce ake gani babbar ƙawa ce ga Isra'ila a karon farko ta nuna damuwar ta a kan yunƙurin na kaka gida, wanda ta ce ba aniya ba ce ta ba da haɗin kai ga sake farfaɗo da shirn wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.An shirya shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel za ta tattauna batun na gina matsugunan Yahudawa tare da fraministan Isra'ila, wanda bisa ga dukkan alamu Jamus ɗin za ta baiyana rashin jin daɗinta ga hukumomin Isra'ilan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal