1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antonio Guterres na shirin zama babban sakataren MDD

October 6, 2016

Zaben sabon magatakardan Majalisar Dinkin Duniya wanda zai maye gurbin Ban Ki-moon wanda wa’adin shugabancinsa ke shirin kawo karshe ana sa ran tsohon firaministan kasar ta Portugal zai lashe zaben.

https://p.dw.com/p/2Qwqo
Antonio Guterres
Hoto: picture-alliance/dpa/J.-Ch. Bott

'Yan takara goma ne dai maza da mata wadanda suka fito daga kasashen duniya daban-daban suka tsaya takarar neman mukamin na babban magatakardan MDD domin maye gurbin Ban-Ki Moon wanda wa'adin jagorancinsa ke shirin kawo karshe. Sai dai kuma tuni alamu suka nunar da cewar  Antonio Guterres tsohon firaministan kasar Potugal  kana tsohon  shugaban Hukumar kula da ‚yan gudun hijira ta MDD ya kama hanyar lashe kujerar Ban-Ki Moon din bayan da kasashe mambobin kwamitin tsaro na MDD 13 daga cikin 15 suka kada kuri'ar amincewa da takarar a wani zaben wucin gadi da kwamitin tsaron ya shirya a jiya Laraba. Bugu da kari manyan kasashen duniya biyar wadanda suka hada da China da Faransa da Amirka da Ingila da Rasha masu hurumin hawan kujerar naki ga zaben nasa dukkaninsu sun ba da goyon bayansu ga takarar tasa bayan da ya gamsar da su a jawabin da ya gabatar

Antonio Guterres
Antonio GuterresHoto: Getty Images/AFP/K. Betancur

.Ya ce  abin da zan yi alkawari a nan shi ne zan yi aiki kafa da kafada da kwamitin sulhu dama kuma na zartarwa  na MDD domin a tare da su mu yi nazarin hanyoyin da suka dace mu bi domin tinkarar matsalar ta'addanci ba wai kan batun yakarsa ba kawai, har da yin nazarin dakile hanyoyin da fasahohin zamani da 'yan ta'addar ke amfani da su wajen aiwatar da miyagun aIyyukansu"

A nan gaba a yau ne kwamitin sulhu na MDD zai gudanar da zaben sabon babban magatakardan MDD a hakumance;kuma ana kyautata zaton cewar takarar tasa za ta samu karbuwa kamar yadda ta kasance a zaben wucin gadin. Tuni dai majalisar tarayyar Turai ta bakin shugabanta Martin Schulz ta bayyana gamsuwarta da zaben Antonio Guterres wanda ya ce ba su da fargabar zai bai wa marada kunya idan aka yi la'akari da aikin da ya yi a baya.