1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

100510 Euro Rettungspaket

May 10, 2010

Ministocin kuɗi na ƙungiyar EU sun kafa wani asusun bayar da gudunmuwa ga ƙasashen ƙungiyar da ka iya samun kansu a cikin matsalar tattalin arziki

https://p.dw.com/p/NKLT
Hoto: bilderbox

A ƙarshen taron da suka kammala a birnin Brussels na ƙasar Beljium ministocin kuɗi na ƙungiyar Tarayyar Turai sun kafa wani asusun bayar da gudunmuwa ga ƙasashen ƙungiyar da ka iya samun kansu a cikin matsalar tattalin arziki.

An kwashe daran jiya ne wakilai na ƙasashe 27 na ƙungiyar Tarayyar Turai suna tabka muhauwaara wanda a ƙarshe suka samu daidaituwar baki akan wani ƙudirin bai ɗaya na kafa wani asusun bayar da tallafi ga duk wata ƙasa ta ƙungiyar da za ta iya fuskantar matsalar ta tattalin arziki da ka iya yin barazana ga faɗuwar darajar kuɗin Euro.

Tsarin dai ya amince da kasafin kuɗi ne na miliyan dubu 750 na kuɗin Euro wanda kuma a cikinsa ne za riƙa ɗauka domin taimakama wata ƙasa ta ƙungiyar da ka iya samun matsala ta kuɗi.

Kashi na farko dai na kuɗaɗen da ya kai miliyan dubu 60 na Euro zai zo ne daga asusun ƙungiyar sannan miliyan dubu 440 na gudunmuwar ƙasashe na ƙungiyar Tarayya Turai, wanda kuma zai samu ƙarin miliyan dubu 250 na Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba da asusun tallafin.

"Wannan tsari zai ƙara ƙarfafa tare da yin kariya ga darajar kudin mu na baye ɗaya, abu ne na musamman ga tarihin Euro da kuma ƙungiyar EU wanda na kan iya cewa al'umma mata da maza cewa muna kare darajar kuɗin jama' a a Jamus ne."

Tuni dai a sakamakon wannan shiri da aka ƙaddamar, darajar kuɗin Euro ta hau a kasuwannin hadadar hannayen jari na Turai da yankin Asiya wanda a ƙasashe da dama kama daga ƙasashen Faransa da Italiya da Danmark da Ingila da Jamus da Spain, darajar kuɗin Euro ta ƙaru.

Reh Olli kwamishinan kula da tsare tsaren kuɗi ne na ƙungiyar.

"Wannan kwararan matakai da ƙasashe menbobin EU suka ɗauka da taimakon kuɗi da hukumar ƙungiyar EU suka bayar haɗe da shawara da babban Bankin Turai ya tsaida sheda cewar zamu yi duk iya kokarimu domin kare daraja takardun kuɗi na euro."

Kusan dai wannan taron dangi da aka yi na futa kuma wanda ya suma manyan bankunan na Turai suka taka rawar gani ya biyo bayan matsalar da ƙasar Girka ta samu kan ta a ciki ne wanda kuma ya so ya yi barazana ga dagula al'amuran kuɗi a nahiyar Turai baki ɗaya, to amma a yanzu da wannan tsari ƙungiyar ba ta shakkar komai.

Josef Pröll ministan kuɗi ne na ƙasar Austriya.

"Yanzu wani lokaci ne mawuyaci ga takardun kudin na Euro harma ga manufofin ƙasashen Turai. Haƙiƙa yanzu wani hali ne mafi tsanani aka shiga a cikin shekaru da dama to amma bai gagaremu warware ba."

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal