1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Iran ta nemi a tallafa wa Falasdinu

Ramatu Garba Baba
May 21, 2021

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nemi kasashen Muslimi da su tashi su taimaka wa Falasdinawa don sake gina yankin da rikici ya ragargaza.

https://p.dw.com/p/3tnVd
Iran Neujahrsansprache Ajatollah Ali Khamenei
Hoto: Office of the Iranian Supreme Leader/Zuma/picture alliance

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kira ga kasashen Muslimi, da su tashi su taimakai Falasdinawa don sake gina yankin da rikicin kwanaki goma sha daya ya ragargaza, Malamin mai karfin fada a ji, ya ce, yanzu ne lokacin da ya dace a nuna musu goyon baya, ta hanyar taimaka musu da makamai ko tallafin kudi, ya ce hakan zai yiwu, idan al'ummar Musulmi sun matsa ma gwamnatocinsu don ganin sun dafa wa Falasdinu da taimakon da suke bukata a yanzu.

A dazun nan, fada ya sake barkewa a wajen Masallacin Al-Aqsa, wurin ibada na uku mafi tsarki ga musulmi a yankin da Isra'ila ke iko da shi a gabashin Kudus, sojojin Isra'ila sun yi amfani da harsasan roba domin tarwatsa Falasdinawan da ke jifansu da duwatsu. Dama masana siyasan duniya, sun baiyana fargabar dorewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin biyu suka cimma da ya kuma soma aiki da safiyar wannan Juma'a a tsakanin Isra'ila da Falasdinawan.