1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan agaji bayan girgizar kasa a China

April 21, 2013

Jami'an aiyukan ceto sun kwashe dare na neman wadanda su ka tsira daga girgizar kasa da ta ritsa da su a yankin kudu maso yammacin kasar China.

https://p.dw.com/p/18KEY
Hoto: Reuters

Dubban masu aiyukan ceto sun yi dirar mikiya a garuruwan da ke yankin kudu maso yammacin kasar China, inda girgizar kasa mai karfi maki 6.6 a wannan Asabar da ta gabata, ta hallaka kusan mutane 200.

Dubban sojojin da aka tura sun kwashe dare su na aikin neman masu sauran nunfashi, kuma firaministan kasar Li Keqiang ya kai ziyara a wajen da abun ya faru, domin ganin yadda aiyukan agajin ke gudana. Akwai wasu mutane fiye da 6,700 da suka samu raunuka sanadiyar girgizar kasar ta China.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar