1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan tallafi kan ilimi a jihohin Arewacin Najeriya

November 30, 2016

 Majalisar Daliban Nigeria ta Arewa kungiya ce da wasu matasa na wasu daga cikin  jihohi 19 ke shugabanta don taimakawa ‘yayan talakawa wajen samun ilimi mai nagarta.

https://p.dw.com/p/2TXYq
Anschlag Nigeria Kano Bayero Universität
Hoto: Reuters

Comrade Safwan Suraji Ilyas ne jagoran kungiyar daliban a wannan tafiya ta kai wa wasu makarantu tallafin da suke bukata a Kano. Kuma ya fadawa tashar DW cewa.

"A Karamar hukumar Madobi mun raba kayayyakin karatu a wata makaranta da ake kira Nurudeen Islamiyya Primary School Madobi. Mun je Kofar Nassarawa Primary School mun bad a kayayyakin karatu da suka hada da  litattafan karatu fensura, biruka da abin goge rubutu  wato cleaner. Sannan idan ka koma  bangaren kayayyaki da suka shafi karatu wato text books kenan, mun je wata makaranta da ake kira Iqra’a Academy, kuma wannan bangaren mun bibiyi matsalolinsu mun gano kayayyaki ne na karatu da suke da bukata”     

A yanzu haka  wannan tallafi dai gamewarsu daga cikin manyan makarantun yankin, wanda zai zama kari ne kan daukar nauyin  kudaden jarrabawar kamala sakandare na wasu matasa da ba su da sukuni.

Akwai mutum goma da muka dauki nauyi wadanda ba su da karfin da za su iya biyan kudin jarrabawa ta SSCE. Mun dauki mutum goma kwarara mun biya musu kudin WAEC.”     

Comrade Safawan wanda ta kan dandalin sada zumunta da muhawara na facebook ya fara ilmintar da matasa, yace da su aka yi gwagwarmaya wajen san'ya harshen Hausa a manhajar ta facebook, yana mai cewa su ma sauran ba za su kyale su ba.   

"To yanzun muntiso Twitter a gaba, mun tiso Whatsapp, su ma sai mun ga sun yi haka. Sannan akwai instagram, shi ma yanzu ana matukar amfani da shi duk da shi hotuna aka fi sakawa. Ba a cika yin dogon rubutu da shi da Twitter

Har yanzu kuwa dandalin na facebbok ne jagora da ‘yan Najeriya ke cin gajiyar abubuwa da daman a kafofin sadarwar zamani, ciki kuwa har da ba da ilimi ba tare da dalibi ya je aji ba, kamar yadda suke a halin yanzu a cewar Comrade Safawan.

“Sai mu dauki littafi sai mu ce yau za mu yi kaza gobe shafi kaza. Ta wannan hanyar  ba sai ka je kasuwa  ka saya ba, ba sai ka je makaranta ba. Wadannan hanyoyi zaka rika karuwa da wannan ilimin. Har irin su Turanci duk za ka ga ana koyawa ‘yan arewa”
 Matasa sama da 200 ne suka amfana da damar da wadannan kafofin yada labarai da sadarwar fasahar zamani suka samar , karkashin kungiyar ma’abota hulda ta kafar facebook cikin su kuwa hard a Malam Mubarak wanda yace.

“A facebook zan iya bayanai na tura. Idan na shawarwari ne na ba da shawara, in tura ni ma. Idan kuma na farin ciki ne da wasu abubuwa na social Nework hakan dai zan yi"