1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Azumin Kiristoci cikin rashin tsaro a Najeriya

Usman ShehuMarch 6, 2014

Kiristoci na yankin Arewa maso gabashin tarayyar Najeriya sun fara azumi na kwanaki araba'in cikin zaman dar-dar sakamakon hare-haren da ke neman zama ruwan dare a yankin.

https://p.dw.com/p/1BLOG
Anschläge auf Kirchen in Nigeria Afrika ARCHIV
Hoto: picture-alliance/dpa

Hare-hare na karuwa a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya. Wannan ma ya sa Kiristoci wannan shiya ke gudanar da azumin bana cikin zullumi. Bishop Oliver Dashe Dome da ke kula da Maiduguri, ya bayyana yadda al-amarin rashin tsaro ke shafan harkokin addinin da suke gudanarwa.

Ba shakka ana kashe-kashe da kone- kone da sauransu, kuma ba shakka ya shafi mambobin kiristoci, ba abin murna ko na farin ciki ba ne. Muna bakin ciki da abubuwan da ke faruwa domin a da, musulmai da kiristoci mu na zamanmu cikin salama. Saboda haka ina karfafa cewa a yi hakuri a bar irin kashe -kashen da ake yi. Idan akwai damuwa sai a zauna a tattauna a ga yadda za'a magance ta".

Oliver Doeme Dashe, Bischof von Maiduguri, Nigeria
Bishop Doeme Dashe na Maiduguri ya yi kira da a zauna lafiyaHoto: DW

Hare-haren kungiyar Boko Haram dai sun fi kamari a karkara fiye da manyan birane, kamar yadda Bishop Dashe ya tabbatar. "Yan uwanmu da suke karkara ana shiga gidaje ana kashe-kashe, ko a gonakai ma ana kashe-kashe, ana kwace amfanin gona sannan kuma mutane suna kan gudu domin ba'a san kowaye zai zo musu, ko da rana ko kuma da daddare ba. Saboda haka abun damuwa ne sosai-sosai, ba abin farin ciki ba ne. Yawancinsu an kokkona musu abinci, amma dai muna gaya musu da su dinga dogaro ga Allah, kuma kada su ce za su rama".

Shi kuwa a nasa bangaren Bishop din Yola, Stephen Mamza ya bayyana irin kokarin da suke yi don hada kan bangaren mabiya addinai ta yadda za'a magance lamarin.

"Ba shakka a kowane lokaci da muke addu'a muna kira ga dukkan kirista da a zauna lafiya da 'yan-uwanmu da suke kewaye damu. Walau musulmi ko kirista ko kuma masu bin addinin gargajiya, dukkaninmu Allah ne ya haliccemu, kuma mu ci- gaba da addu'a don babu abin da yafi du'a'i"

Nigerien Maiduguri Autobombe Doppelanschlag März 2014
Ana ci-gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Biship Mamza ya kuma yi kira ga Kiristoci da su yi amfani da wannan azumin, domin yin addu'ar samun saukin tashin hankali a yankin. "Muna godiya ga Allah da ya bamu zarafi har muka fara azumin wannan shekara. Jiya muka fara azumin Laraba na tuka, mun san cewa a yankin Borno da Yobe da Adamawa, muna fama da matsalolin tsaro. Don haka za mu yi addu'a Allah ya bamu zaman lafiya, ga sojoji da ke aiki domin tsaron lafiya anan a kasarmu.

Tashe-tashen hankulan dai sun tsananta a makwannin da suka gabata a Jihohi uku da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wadanda suke karkashindokar ta-baci.

Mawallafiya: Zainab Babbaji
Edita: Mouhamdou Awal Balarabe/USU