1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baƙin hauren Afirka a Turai

August 31, 2009

Tsauraran matakan da Italiya ta ɗauka na tsaron kan iyakokinta na ruwa ga ´yan gudun hijira na saka rayukansu cikin haɗari

https://p.dw.com/p/JMZd
´Yan gudun hijirar Afurka a tsibirin LampedusaHoto: AP

Kimanin makonni uku cir suka yi suna watangaririya kan tekun-bahar rum, inda saba'in da uku daga cikinsu suka yi asarar rayukansu. Wannan maganar ta shafi wasu 'yan gudun hijira ne daga ƙasashen Eritrea da Habasha da Nijeriya ta suka taso daga Libiya a ƙoƙarin shigowa nahiyar Turai a cikin wani ɗan ƙaramin kwale-kwale. Wannan tsautsayin na ɗaya daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afurka a wannan mako. A lokacin da take sharhi game da haka, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"A sakamakon tsauraran matakai da ƙasashen Turai ke ɗauka na tsaron gaɓoɓin tekunsu 'yan gudun hijirar ke daɗa ɗaukar matakai masu haɗarin gaske a game da makomar rayuwarsu. Ita kuma ƙungiyar 'yan gudun hijira ta MƊD ta ce ta lura a baya-bayan nan cewar da yawa daga kaftin-kaftin na jiragen ruwa da kan ci karo da 'yan ƙananan kwale-kwalen dake ɗauke da 'yan gudun hijira ba sa ma sanar da jami'an tsaro ko da kuwa suna fuskantar haɗarin gaske, sai su yi ko oho da su. A yanzu tekun-bahar rum ta zama wani dandali na iya ruwa fid da kai."

A wani sabon ci gaba da ake samu a Afurka, gaggan kamfanoni daga ƙasashe masu arziƙin masana'antu na sayar filayen noma masu danshi daga hannun talakawa, in ji jaridar Frankfurter Rundschau, wadda ta ci gaba da sharhi tana mai cewar:

"An shiga wani sabon yanayi na hadama a nahiyar afurka, inda 'yan kasuwa na ƙetare ke sayar filaye masu albarkar noma domin lafar da matsalar yunwa a ƙasashensu. Waɗannan masu wawason filayen da suka haɗa da manyan kamfanoni da bankuna da gwamnatoci na ƙetare ga alamu basa ƙoshi. Domin kuwa alƙaluma sun nuna cewar an sayar da filin noma da ya kama kimanin eka miliyan 20 a nahiyar Afurka tsakanin shekara ta 2006 zuwa yanzu, abin da ya sanya ƙungiyar abinci da noma ta MƊD ke batu a game da wani sabon salo na mulkin mallaka."

A ƙasar Mali ɗaruruwan mutane suka shiga zanga-zangar adawa da wata dokar ƙarfafa haƙƙin mata a ƙasar. A lokacin da take bayani game da haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Wasu daga cikin masu zanga-zangar su nuna fushi matuƙa ainun, inda suke nuna adawarsu da abin da suka kira wata dokar da zata kawo rarrabuwa tsakanin al'umar ƙasar. To sai dai kuma wannan adawa tana da ban mamaki ganin yadda dokar ta samu cikakken goyan baya a majalisa, inda wakilai 117 suka ba da goyan baya a yayinda biyar kacal suka ƙi amincewa da wannan doka. Wasu daga cikin masu zanga-zangar na adawa da dokar ne saboda a ganinsu tayi daura da shari'ar musulunci."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal