1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaro na ci gaba da farautar maharan Paris

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 19, 2015

Rahotanni daga kasar Faransa na nuni da cewa har kawo yanzu ba a kai ga gano inda wadanda ake zargi da kitsa harin da aka kai a birnin Paris na kasar ba.

https://p.dw.com/p/1H8hy
Abdelhamid Abaaoud wanda ake zargi da kitsa harin Paris
Abdelhamid Abaaoud wanda ake zargi da kitsa harin ParisHoto: picture-alliance/dpa

Bayannan da ke fitowa daga kasar sun tabbatar da cewa daga cikin mutane bakwai da jami'an tsaron Faransan suka yi nasarar cafkewa a wannan Larabar, babu Abdelhamid Abaaoud da kuma Salah Abdeslam, wadanda aka hakikance suna da hannu a harin na birnin Paris da ya hallaka mutane 129. A kallah mutane biyu ne suka mutu a yayin samamen da jami'an tsaron suka kai wani gida a yankin Saint Denis da ke kusa da birnin na Paris, ciki kuwa har da wata mace da ta tayar da abubuwa masu fashewa a jikinta yayin da dayan kuma ya mutu sakamakon harbin bindiga. Jami'an tsaron dai sun cafke mutane bakwai a yankin na Saint Denis a yayin wannan samame.