1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba tabbas bisa makomar siyasar Burundi

Abdourrahman HassaneJune 25, 2015

Kwanaki hudu a gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki a Burundi Rufyikiri ya arce daga kasar zuwa Beljium tare da yin kira ga shugaba Pierre Nkuruziza ya manta da yin ta-zarce

https://p.dw.com/p/1FnUU
Bujumbura Burundi Protest Gewalt
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Gervais Rufyikiri wanda ya ware zuwa birin Liege na Beljium mallamin jami'a ne kwararre wanda kasashen duniya ke yabawa da yadda yake yin aiki saboda tsatsaura ra'ayinsa ya taba zaman shugaban majalisar wakilai a lokacin wa'adi na farko na shugaba Nkurunziza daga shekarun 2005 zuwa 2010 kafin daga bisanin a nada shi mataimakin shugaban kasar na biyu bayan an sake zaben shugaban kasar a wa'adi na biyu.

Mista Rufyikiri ya ce ya fice daga Burundi ne domin ba zai iya ci gaba da goyon bayan shugaba Pierre Nkuruziza ya yi takara ba, ba a ka kaida ba a zaben shugaban kasar da za a gudanar a nan gaba a ranar 15 ga watan Yuli, ya kuma shaida wa tashar DW cewar tun lokaci da ya kafe a kan matsayinsa aka fara yi masa barazana

''Ya ce na fuskanci bita da kuli a cikin Burundi inda a wani lokacin bani da cikakken iko ko izini na bayyana ra'ayina, tare da na da wasu sauran jama'ar wadanda muka bayyana matsayinmu a kan zaben tun cikin watan Maris a ya gabata, ya ce mun fuskanci wariya da wulakanci har ma da barazana ta kisa.''

Burundi Proteste gegen Präsident Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay
Burundi Vize-Präsident Gervais Rufyikiri
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Da wannan arecewa da da Gervais Rufyikiri ya yi daga Burundin , addadin 'yan kasar ta Burundi wadanda aka tilasta wa yin hijira kama da 'yan jarida da kungiyoyin fara hula da kuma manbobin jam'iyyar da ke yin mulki wato CNDD sun karu.

Domin ko yanzu wasu na kusa da wani mataimakin shugaban kasar na Burundi Bernard Busokoza na furta kalamun cewar shi ma ya tsere zuwa kasar Beljium a yau Larba, yayin da wasu rahotannin da ba a tabbatar da gaskiyyarsu ba ke cewar mai yi wa shugaban majalisar dokokin mai barin gado wanda shi ma ke nuna adawa da takara ta Nkurunziza ya ranta cikin na kare Gervais ya ce ba su ka dai ba na a kwai jama'a da dama da ke da niyar barin kasar