1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babangida ya bayyana niyyarsa ta yin takara.

August 16, 2010

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida zai tsaya takarar zaɓen shugaban ƙasa na baɗi.

https://p.dw.com/p/OokB
Taswirar Najeriya.Hoto: AP Graphics

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya sanar da niyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen baɗi. A wata sanarwa da kakakinsa ya bayar a yau, Babangida ya ce zan gudanar da yancina ne, tun da jam'iyyarmu ta amince ga duk mai buƙata ya fito. Sanarwar da Babangida ya bayar a yau, wani babban koma bayane ga shugaba Jonathan da masu sun tsai da shi shugabancin ƙasar a zaɓe mai zuwa. Janar Babagida dai ya shugabancin Najeriya na tsawon shekaru kusan takwas, kafin ya miƙa wa gwamnatin riƙon ƙwarya, ya koma Minna a jaharsa ta Niger. Shi ma dai tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, a jiya ne ya ayyana neman shugabancin ƙasar ƙarƙashin lemar PDP. Da ma dai a kundin tsarin mulkin jam'iyyar tasu ta PDP, sun amince da mulki ya riƙa zagawa tsaknin kudu da arewa, domin yi wa ko wane ɓangare adalci kamar yadda jam'iyar ta cimma, hakan kuwa yana nufin yankin arewacin ƙasar ne zai fid da shugaba, idan dai za abi tsarin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas