1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Islamkonferenz Streit

May 18, 2010

Zagaye na biyu na babban taro kan addinin Musulunci a Jamus ya mayar da hankali kan inganta cuɗanya tsakani

https://p.dw.com/p/NRFh
Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere lokacin buɗe zagaye na biyu na babban taron addinin Musulunci a BerlinHoto: picture alliance/dpa

Bayan shekaru masu yawa ba a gana da juna tsakanin Musulmai da ke zama a ƙasar Jamus, yanzu an fara ɗaukar matakai na ƙarfafa cuɗanya tsakanin ɓangarorin, inda a yanzu ƙasar Jamus take da Musulmai kimanin miliyan huɗu. Don haka nema aka gudanar da taron musulunci a birnin Berlin, inda ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya jagoranci tattaunawar.

Taron dai ya samu halartar ƙungiyoyi da al'umar Musulmai kama daga na tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi na ƙasar ta Jamus, inda kuma suka tabka muhauwarori, kan batutuwa masu yawa da suka shafi rayuwar Musulmai a ƙasar. Ministan cikin gida Thomas de Maiziere ya bayyana matuƙar gamsuwarsa bayan da ya fito daga zauren muhauwarar.

"Mun yi ƙyaƙƙyawar tattaunawa, kuma zan iya kwatanta ta da muhauwara ce mai gamsarwa, wadda ta fi mayar da hankali kan dukkan abin da ya shafi al'adu. Maganar da tsohon ministan harkokin cikin gida Wolfgang Schäuble ya yi na cewa Musulunci yanzu ya kasance wani ɓangare na Jamus, ma'ana ba baƙon abu ba ne, kuma nima na ƙara jaddada goyon bayana a kai. Kana a bisa hakan zamu ɗora aikin mu."

Wannan taron dai an gudanar da shi ne ba don wa'azi ko muƙabala ba, amma manufarsa shi ne a samu tattaunawa ta fahimtar juna, da samun yarda da juna tsakanin al'ummar Musulmai dake zama a Tarrayar Jamus. Kamar yadda ministan cikin gidan ya ƙara da cewa.

"Da farko dai muna son mu horar da limamai sabon tsarin zamani da kuma walwala ta al'adun ƙasar. Abin da muke son Musulmai su koya a darussan, shi ne su san al'adu da tsarin ƙasa, kuma wannan zamu yi shi ne a dukkan faɗin tarrayar Jamus, abin da zamu iya yi kenan."

Su ma kansu mahalarta taron sun bayyana jin daɗinsu game da muhauwarar, domin suna ganin idan da ana zama da juna irin haka to al'amura da sun fi haka tafiya. Hamid Abdu-Samad masanin kimiyyar siyasa da ya halaraci taron.

"Ina mai matuƙar farin ciki, da yadda muhauwarar ta kasance, kuma ta yi nasara. Abu na farko shi ne ƙaKKyawar labarin."

Ministan kula da cuɗanyar al'umma na jahar Nordrhein-Westfalen, ya bayyana farin cikinsa, inda ya ce wannan shi ne karo na farko da aka samu zama a teburi ɗaya tare da ƙungiyar Musulmai ta biyu mai girma a nan Jamus wato ta Bosniyawa, tare da 'yan ƙasar Moroko da Turkawa. Don haka ministan ya ce wannan abu ne dake nuna an samu nasara.

Yanzu dai ministan cikin dan Jamus ya bayyana cewa za'a sake irin wannan taron cikin wannan shekara, ko kuma farkon shekarar baɗi.

Mawallafa: Sabine Ripperger / Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal