1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron jam'iyyar kwamunisancin Sin

November 8, 2012

Shugaban ƙasar Sin ya yi gargadin cewar muddin ba a kau da cin hanci da kuma kara bunkasa tattalin arzikin kasar ba, to jam'iyyyar kwamunisancin kasar za ta ruguje.

https://p.dw.com/p/16fH3
Hoto: REUTERS

Shugaba Hu Jintao ya ambata hakan a Alhamis ɗin nan lokacin da ya yi wani jawabi da ya yi lokacin da ya buɗe babban taron jam'iyyarsa, inda ya ce muddin ba su tashi tsaye wajen shawo kan matsalar ba to shakka babau jam'iyyar za ta iya fuskantar matsalar da ba za su iya warware ta ba.

Mr. Hu ya ƙara da cewar dole su cigaba da kasance masu ƙwazo da riƙon amana duba da ƙudurin da su ka ɗauka na son yin gyare-gyare ga tsarin siyarsa su domin kaiwa ga nasara.

Wadannan kalamai na shugaban na kasar ta Sin na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ke shirin zaɓen sabbin shugabaninta da ma dai batun cin hanci da rashawa da ya yi wa jam'iyyar dabaibdayi.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe