1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron Jam'iyyar ZANU-PF

Yusuf Bala/ASDecember 2, 2014

A cikin makon nan ne jam'iyya mai mulki a Zimbabuwe wato ZANU-PF za ta zabin sabbin shugabanni da za su ja ragamar jam'iyyar tsawon shekaru shidda da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1DyAc
Zimbabwe Robert Mugabe
Hoto: Reuters

Taron jam'iyyar ta ZANU-PF na cigaba da jan hankulan al'ummar wannan kasa, inda da dama ke fatan ganin sauyi kan wanda za su ja ragamar jam'iyyar kon samun sauyi kan yadda ake tafiyar da kasar yayin da wasu a gefe guda ke ganin da wuya wannan buri na jama'a ya samu duba da yadda 'yan amshin shata na Shugaba Mugabe suka kankange abubuwa a jam'iyyar.

Joyce Mujuru
Joyce Mujuru na cikin tsaka mai wuya duba da irin adawar da ta ke fuskanta a jam'iyyarHoto: picture-alliance/AP Photo

Dr. Pedzisai Ruhanya mai sharhi da ke kan harkokin siyasar kasar ta Zimbabuwe na daga cikin masu tunanin ba za ta sauya zani ba dangane da wanda za su jagoranci jam'iyyar inda ya ke cewar "taron barazana ce kasancewar wannan yunkuri babu abinda zai haifar wajen samar da makoma ta gari ga harkokin tattalin arzikin kasar ta Zimbabwe. Shugaba Mugabe zai sake gadon kansa da kansa ne kawai".

A daura da wannan wasu kuwa na kallon cewa makomar siyasar mataimakiyar shugaban kasar Joice Mujuru ce za ta shiga cikin hali na tsaka mai wuya duba da yadda aka hana ta shiga don neman a fafata da ita wajen neman matsayi. A da dai ana mata kallon wacce za ta gaji Mugabe, sai dai mai dakin shugaban na zarginta da rashin iya tafiyar da mulki yayin da ake kallonta a matsayin mai kokarin kawar da shugaban kasar ko ta halin kaka.

Wannan halin da ake ciki na gaba kura baya siyaki a jam'iyyar ta ZANU-PF ya sanya mutane irin Lameck Showi bayyana damuwa kan abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar inda ya ce "ina ganin taro ya yi abinda zai yi, munga yadda aka fitar da mutane daga kwamitin zartarwa. Mun kuma ga inda matar shugaban kasa ta sanya gabanta, saboda haka dama babu wani abu sabo da muka zaci gani daga wannan taro".

Grace Mugabe
Alamu na nuna cewar Grace Mugabe na yunkurin gadon mijinta in ya bar mulkiHoto: picture-alliance/dpa

A ranar Laraba ne dai masu fada aji a jamiyyar za su yi wani zama dan duba yadda za a samar da sauye-sauye a kundin tsarin mulkin jam'iyyar ta yadda Mugabe zai iya daukar mataimakiyar sa dama matsayar shugabancin jam'iyyar ta Zanu PF.