1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakalar shaidar karatun jabu ga ministar jiragen saman Najeriya

January 9, 2014

Kungiyoyin kare hakkin jama'a a Najeriya sun bukaci ministar sufurin jiragen saman kasar Stella Oduah ta koma gefe domin binciken zargin mallakar takardun karatun boge.

https://p.dw.com/p/1AoKm
Nigeria Präsident Goodluck Jonathan
Hoto: picture-alliance/dpa

Bankado cewar ana zargin ministar kula da harkokin sufurin jiragen saman Najeriya Stella Oduah na mallakar takardun digiri na boge kan ikirarin da ta yi cewar tana da digiri na biyu daga jami'ar Saint Pauls da ke Virginia a kasar Amirka, tuni ya sake takalo batun abin kunyar da ke shafar sahihancin takardun da wasu masu rike da mukaman siyasa kan yi ikirari, wanda kuma ya zama lamarin da ke ci gaba da tada jijiyar wuya saboda matsayin da take rike dashi.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a da suka yi gaba wajen bayyana damuwarsu a kan wannan batu da suka ce ya shafi batun alkawarin aikata gaskiya ga ministar ta Najeriya, sun ce dole ne a dauki mataki na sadidan domin kauwacewa sake afkuwar hakan. Malam Sani Aliyu shi ne shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Gacoal a Najeriya.

‘'Ai yadda ake zarginta da irin wadannan abubuwa, ba wai sai ta jira an ce mata ta janye ba, kamata ya yi ta sauka daga mukaminta kawai, amma in ba za ta yi haka ba abin da muke kira ga masu bincike a kan harkar cin hanci da rashawa shi ne su kama ita wannan ministar, ko kuma su sanyata ta sauka daga mukaminta, domin abin da ya samu irin su Salisu Buhari tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya, ita ma ya sameta''.

Sicherheitstreffen Nigeria
Shugabannin rundunonin tsaro a NajeriyaHoto: DW

Gaza hukunta masu laifi ne ke karfafa wa wasu gwiwa

Ma'aikatar kula da sufurin jiragen saman Najeriya dai ta ki cewa uffan a kan wannan batu, domin kuwa Mr. Yakubu Datti, mai magana da yawun hukumomin da ke karkashin sufurin ya ce ba za su ce uffan ba.

Kama dai daga tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriya Salisu Buhari zuwa ga tsofaffin gwamnoni a jihohin Legas dama Benue, batun zargin mallakar takardu na boge ya zama ruwan dare ga ‘yan siyasar Najeriya da suka mayar dashi abin ado, don a ce su kai wani matsayi. Wannan ya sanya Dakta Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da zamantakewar bani adama da ke jami'ar Abujan Najeriya bayyana illar da ke tattare da hakan.

‘'Wannan wata hallaya ce ta ‘yan siyasar Najeriya musamman ma dai a wannan zamani su dage cewa sai sun birge ko su wata tsiya ce bayan kuwa su din ba wata tsiya bace. Wannan abin ya ci gaba ne saboda har yanzu ba'a dauki wani kyakkyawan mataki na darasi a kan wani ba, domin in baya ga shi Salisu Buhari da ya rasa mukaminsa, ai babu wani wanda aka hukunta shi. Watau za'a ci gaba da samun irin wadannan abubuwa matsawar a duk lokacin da aka fallasa cewa wani ya yi karya kuma aka kyaleshi ya tafi abinsa, domin mutumin da zai fito ya yi karyar cewa yana da wani abu kuma alhali baya dashi sannan yana rike da wani mukami, to ai ka ga bama isgilanci ba, ya ma karya mutuncin wannan mukamin nasa."

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Ginin majalisar dokokin NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Bayanai dai sun nuna cewa tuni ministar ta cire takardun da take dasu wadanda aka sanya a shafin yanar gizo na ma'aikatar, to sai dai da alamun an yi shufka a idon makwarwa domin akwai wadannan takardun a jerin wadanda aka baiwa majalisar dokokin Najeriya.

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Saleh Umar Saleh