1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baki 'yan kakagida a zaben Jamus

September 4, 2013

Mutane fiye da miliyan biyar masu asali daga kasashen ketare na da 'yancin kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin Jamus da zai gudana a ranar 22 ga watan Satumban 2013.

https://p.dw.com/p/19W8i
Kuri'ar zaben Jamus
Kuri'ar zaben JamusHoto: Fotolia/MaxWo

Shin wa za su kada wa kuri'a har in sun yanke shawarar zuwa rumfunan zabe don sauke wannan nauyi? Wannan dai zai dogara ne ga ra'ayinsu da ma tarihin kasashensu na asali.

Juan Diaz Ba-Amirke ne mai asali daga kasar Kuba wanda iyayensa suka tsere daga Kuba karkashin gwamnatin Fidel Castro zuwa birnin Miami dake jihar Florida ta Amirka. Tun shigowarsa birnin Berlin ya so birnin saboda yawan al'ummomi daga sassan duniya daban-daban dake a babban birnin na tarayyar Jamus. Tun kimanin shekaru bakwai da suka wuce Juan Diaz ya karbi fasfo din Jamus.

"Na nemi zama dan kasa domin na san zai bani 'yancin fadin albarkacin baki na da kuma damar shiga a dama da ni musamman a zaben shugaban gwamnati da na 'yan majalisar dokoki, wanda yanzu nake da izinin yi."

Berlin: Ankunft deutschstämmiger Aussiedler mit Gepäck und großen Taschen auf dem Berliner Flughafen Schönefeld. Die Zahl der Spätaussiedler ist im August auf den niedrigsten Stand seit 1987 gefallen. Im vergangenen Monat wurden 10671 Aussiedler in der Bundesrepublik registriert. Im selben Monat des Vorjahres waren es rund 14 600 und 1995 gut 18100. Mit 94159 Personen kamen in den ersten Monaten dieses Jahres fast 20000 Spätaussiedler weniger als im Vergleichszeitraum 1996. Die meisten Menschen kommen noch immer aus der ehemaligen Sowjetunion, teilte das Bundesinnenministerium am 01.09.1997 in Bonn mit. (BER422-300997) Für: Projekt Destination Europe : Mangelnde Perspektiven und große Träume
Hoto: picture alliance/ZB

Son jam'iyya ya danganta da kasar da bako ya fito

Kididdigar da ofishin kididdiga na tarayya ya gudana a shekarar 2011 ta nuna cewa mutane kusan miliyan 16 a Jamus wato irinsu su Diaz ke da asali daga ketare wato ko dai don radin kansu suka bar kasashensu ko kuma iyayensu ko kakannensu ne suka yi kaura zuwa Jamus. Akasarinsu ko dai yara ne da ba su kai shekarun kada kuri'a a kasar ba ko kuma ba su da takardun zama Jamusawa. Domin mai rike da fasfo din Jamus kadai ne ke da 'yancin kada kuri'a a zaben kasar, in ban da 'yan kasashen tarayyar Turai wadanda doka ta ba su damar kada kuri'a a zabukan kananan hukumomi da na 'yan majalisar Turai ko da ba su da fasfunan Jamus ne, amma ba sa iya zabe na majalisar Bundestag.

Alkalumman ofishin kididdiga na tarayya sun nuna cewa kashi daya cikin uku na Jamusawa masu asali daga ketare za su kada kuri'a a zaben majalisar dokoki ta Bundestag a watan Satumba. Sai dai wani bincike ya nuna cewa wannan rukuni na Jamusawa masu tushe daga ketare ba safai suke kada kuri'a ba idan aka kwatanta da Jamusawa tsantsa. Amma Juan Diaz Ba-Amirken Jamus mai asali daga Kuba ya ce shi kam zai sauke wannan nauyi.

"Abin sha'awa ga Jamus shi ne ba ka bukatar zama dan wata jam'iya kafin ka yi zabe. Ina ganin Amirka za ta koyi darasi daga wannan. Ina jin dadi a duk lokacin da na samu katin zabena dake cewa in tafi in kada kuri'a, 'yancinka ne na demokradiyya."

Masaniya kan asalin kasa na da muhimmanci

Ingrid Tucci, Sozialforscherin am DIW. Copyright: privat
Ingrid Tucci masaniyar zamantakewar jama'aHoto: privat

Masu zabe irinsu Diaz sau da yawa sun fi zaben manyan jam'iyyu kamar SPD ko CDU, inji Ingrid Tucci ta cibiyar nazarin tattalin arzikin Jamus, wadda kuma ta gudanar da bincike kan jam'iyyun da bakin suka fi yi wa biyayya.

"Baki ma'aikata sun fi karkata ga SPD, wato 'yan kwadagon da bisa al'ada suka yi kaura zuwa Jamus. Sannan su kuma 'yan asalin Jamus da suka dawo kasar ko baki daga gabacin Turai sun fi kaunar CDU."

Masaniyar ta ce batun kyautata zamantakewar al'umma na taka rawa a nan. Domin idan aka dubi batun 'yan asalin Jamus da suka dawo kasar za a ga cewa CDU ta yi musu kokari wajen saukaka judanyarsu da 'yan kasa, amma ana fassara take-taken wasu daga wakiltanta da cewa kyama ce ga baki ma'aikata.

Mawallafa: Naomi Conrad / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani