1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ban Ki-moon ya yi murna ga sabon jagora

October 6, 2016

Guterres da zai karbi Mista Ban a Majalisar Dinkin Duniya ya sha alwashi na fuskantar kalubale da ke zame wa duniya kadangaren bakin tulu, wato rikice-rikice kala daban-daban.

https://p.dw.com/p/2Qz4m
Schweiz Genf Antonio Guterres
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Di Nolfi

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a hukumance ya zabi tsohon Firaministan Potugal Antonio Guterres a matsayin wanda zai maye gurbin Ban Ki-moon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a nan gaba.

Da yake jawabi bayan bayyana shi a matsayin wanda zai karbi wannan babbar kujera a birnin Lisbon, Guterres cikin kaskantar da kai ya nuna godiyarsa.

"Abin da na ke ji a yanzu shi ne ina bukatar kalmomi guda biyu ne jin an mutunta ni da godiya. Godiya ga wadanda suka zabe ni yadda Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zabe ni da samun karfin gwiwa a kaina, da kuma godiya baki daya ga taron majalisar da mambobinta, sannan ina godiya ga sauran abokan takarata wadanda rawar da suka taka a lokacin neman wannan kujera ya kara fito da kimar wannan majalisa."

A karshen wannan shekara ne dai Ban Ki-moon zai kammala wa'adin mulkinsa a majalisar inda tuni ya taya abokin gwagwarmayarsa murna.