1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Banayi kan rikicin kyamar baki a Afirka ta Kudu

Suleiman BabayoJune 3, 2015

Rikicin kyamar baki za a iya dangantawa daga yadda 'yan Afirka ta Kudu suna zauna karkashin mulkin nuna wariyar launin fata

https://p.dw.com/p/1FbRq
Gewalt gegen Einwanderer in Johannesburg
Hoto: picture alliance/dpa/K. Ludbrook

Farfesa Abdullahi ashafa malami a Jami'ar Jihar Kaduna ta Najeriya ya yi mana bayani kan abin da ke janyo rikicin a kasar Afirka ta Kudu da ake kai hare-hare kan 'yan kasashe ketere. Malamin ya nunar da cewa 'yan Afirka ta Kudu sun dade karkashin mulkin nuna wariyar launin fata lokacin mulkin Turawa tsiraru. Kuma bayan kawar da gwamnatin nuna wariyar Shugaba Nelson Mandela ya fito da mulkin hadin kan kasa, amma bakeken fata tun daga lokacin suka fara nuna wa bakin bakake wariya. Yayin da sauran bakake suke ganin sun taimaka wajen samar da 'yanci ga 'yan kasar.

Malamin ya kara da cewa dalilin tattalin arziki na kan gaba saboda galibi baki suna aiki, yayin da marasa aiki 'yan kasar ke gani an kwace musu guraben ayyuka. Daga karshe malamin ya nemi gwamnatin AFirka ta Kudu ta tashi tsaye wajen samar wa matasa da aiki.