1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana ga ma'aikatan agaji a Niger

August 20, 2010

Kungiyoyin taimako na ketare sun janye daga yankunan Niger saboda dalilai na tsaro

https://p.dw.com/p/OsR1
Rabon abinci ga masu bukata a NigerHoto: WFP

To jaridun na Jamus a wannan mako sun rubuta sharhuna masu tarin yawa game da nahiyar mu ta Afrika, tun daga sakamakon zaben kasar Rwanda da halin da ake ciki na rashin tsaro a Somalia da batun yunwa dake barazana a jamhuriyar Niger.

A baya-bayan nan batun gurbacewar ruwa a tekun Mexico, inda wani dandalin hakar man fetur na kamfanin BP ya nutse ya dauki hankalin duiya baki daya. To amma a yayin da aka sami nasarar shawo kan wannan yanayi, aka kuma shiga daukar matakan tsabtace inda hadarin ya faru, a wasu yankunan duniya, ana ci gabada samun gurbacewarf muhalli ba tareda an maida hankali a kansa ba. Jaridar Berliner Zeitung tace idan mutum ya duba abin dake faruwa a yankin Niger Delta, zai yi wuya a yarda da cewar wnanan yanki shine tushen dimbin arzikin da Nijeriya take dashi. Ruwan teku a waanan yanki ya gurbace da man fetur, tsirrai da sauran halittu duk sun mutu, kasar wurin ta lalace. A yankin dai babu makarantu ko asibitoci ko hanyoyi ko ruwan sha mai tsabta. Tsakanin shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2009, gwamnatin Nijeriya tayi kiyasin an sami hadarin gurbacewar ruwan Niger Delta daga man fetur abinm da ya kai sau 2400. Ba abin mamaki bane, inji jaridar da kungioyoyi na yan tawaye kamar MEND suke cin karen su ba babbaka a can.

Kasar Niger tana fuskantar barazanar fadawa hali na yunwa, inda gwamnati take kira ga neman taimako daga kasdashe da kungiyoyin duniya. To amma a yayin da irin wadannan kungiyoyi suke bada gudummuwa, suna kuma fuskantar barazanar sakamakon rashin tsaro a yankunan da suke. Hakan ya sanya a wannan mako, kungiyoyin na agaji suka sanar da cewar sun janye ma'aikatan su daga wasu yankuna na kasar domin tsaron lafiyar su. Dangane da haka, jaridar Die Tageszeitung tace shirin da aka kaddamar a yanzu, na taimakawa masu fuskantar bala'in yunwa a yankin Sahel na Niger, zai zama tilas a dakatar dashi. A birnin Niamey, kakakin hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya, yace hukumar ta janye ma'aikatan ta daga Maradi da Zinder saboda dalilai na tsaro. Ba ma ita wannan kungiya kadai ba, inji jaridar Die Tageszeitung, sauran kungiyoyi ma suna shirin kwashe ma'aikatan su saboda tsoron aiyukan kungiyar al-Qaeda ta yankin Maghreb.

A kasar Rwanda an yi zabe an gama, kuma shugaban kasar mai ci, Paul Kagame, kamar yadda aka yi zato shine ya sami nasara. to sai dai jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben aka kai hari mai tsanani a tsakiyar birnin Kigali, inda mutum daya ya mutu, wasu da dama suka sami rauni. Jaridar Tageszeitun tace wnanan hari tilas Kagame ya fahimce shi a matsayin amsa ta siyasa daga abubuwan da ya rika fadi lokacin kampe, inda yace yayi imanin al'ummar Rwanda gaba daya suna bayan sa. Wannan hari ya nuna cewar ba dukkanin yan Rwanda din ne suka amince da manufofin sa ba. Tun ma kafin zaben, sai da aka dauki matakin kama manyan yan adawa ko kuma aiwatar da kisa kan wasu da suka ki mika kai bori ya hau.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhi ne a game da halin siyasa da ake ciki a Zimbabwe. Tace wadanda ke tafiyar da mulki a kasar, sun fara tunain yadda zasu tsara rayuwar su da rayuwar kasar bayan shugaba Robert Mugabe ya wuce. Watanni goma sha takwas bayan nada gwamnatin hadin kan kasa, tare da Morgan Tsvangirai a matsayin Pirayim minista ZImbabwe ta tsaya gaba daya, kuma babu alamun wani abu zai faru kafin zaben da aka shirya yi a tsakiyar shekara mai zuwa. Batun zaben na Zimbabwe shine ma babban abin da aka maida hankali kansa a lokacin taron kolin kasashen hadin kan tatalin arzki na yankin kudancin Afrika, wato SADC a Windhuk, babban birnin kasar Namibia. Wannan hali na rashin ci gaba a Zimbabwe, inji jaridar FAZ, yana tsoratar da masu zuba jari daga ketare, inda a bara jarin ketare da ya shiga kasar bai wuce na dolar miliyan 60 kawai ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar