1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar barkewar yaki a gabashin Kwango

Salissou Boukari
June 28, 2017

Gwamnan yankin Kivu a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango Julien Paluku ya sanar da yuyuwar barkewar yabon yaki a kasar, inda ya yi kira ga sojoji da su dauki matakai, kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/2fZ92
Kongo - Operation gegen die ugandischen Rebellen der ADF-Nalu
Mayaka 'yan tawayen Uganda a KwangoHoto: Reuters/Kenny Katombe

Cikin wani jawabi da ya yi a gaban manema labarai, gwamnan na Kivu Julien Paluku ya ce ya yi wannan tsokaci ne don ganin rundunar sojojin kasar ta dauki batun da babban mahimmanci ta yanda za ta fuskanci lamarin da ke ci gaba da bada tsoro. Gwamnan ya kara da cewa, yawaitar hare-haren ta'addanci a yankin Beni ya fuce karfin wanda ake zargin mayakan Maï-Maï da aikatawa, inda ya ce da alama akwai wasu mayaka na boye da bincike ne kawai zai iya gano su. Da sanyin safiyar yau din nan ma mayakan da ake zargi 'yan Maï-Maï ne sun kai hari ga sojojin kasar ta Kwango a yankin Kalau sai dai ba tare da an samun rasa rayuka ba a cewar wani babban jami'in sojojin kasar.