1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar fadada rikicin Mali zuwa sauran nahiyar Afirka

January 18, 2013

Faransa ta shiga yaki mai sarkakiya a kasar Mali a yunkurin kawo karshen mamayewar da kungiyoyin musulmi suke ci gaba da yiwa arewacin kasar

https://p.dw.com/p/17Mrh
Hoto: Getty Images

A game da nahiyar Afirka, jaridun na Jamus gaba daya sun maida hankalinsu ne kan al'amarin dake daukar hankali yanzu a nahiyar, wato rikicin kasar Mali da yadda zai shafi zaman lafiya a wannan nahiya.

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta rawaito cewar ko da shike Faransa ta sami goyon baya da amincewa daga dukkanin bangarori, amma tilas ne ta shimfida tsarin yadda take son samun nasara a yakin da ta tsunduma kanta ciki a Mali. Lokacin da shugaban Faransa Francois Hollande ya sanar da tura jiragen saman yakin kasar suka fara jefa bama-bamai kan mayakan yan tawayen na Mali, burin Faransa shine ta dakatar da yunkurin yan tawaye na mamaye kudancin Malin. Ko da shike Faransa din ta sami nasarar hakan, amma nan da nan yan tawayen suka fadada rikicin, har yadda ya zama tilas Hollande ya kara yawan sojojin sa a Mali,ya kuma tura mayaka na kasa.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace ana iya ganin saikamakon fadada wannan yaki da yan tawayen suka yi sakamakon abin da ya faru a kasar Aljeriya, inda yan tawaye ke tsare da dimbin baki yan kasashen ketare, kuma a yunkurin kwato su, akalla hamsin suka rasa rayukansu, tare da alkawarin ci gaba da kashe sauran da suka rage a hannunsu, muddin Faransa bata dakatar da yakinta a Mali ba. Jaridar Die Welt ta tabo mummunan sukan da kasashen duniya suke yiwa jami'an tsaro na Aljeriya ne, saboda yunkurin da suka yi ba tare da wani shiri sosai ba, domin kwato yan kasashen ketare dake hannun yan tawayen da suka yi garkuwa dasu a wata masana'anta ta samar da gas a hamadar kasar, inda mutane da yawa suka mutu. Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron na Aljeriya basu sami nasarar kwato wannan sansani gaba dayansa daga hannun yan tawayen ba, yayin da shugabanni a kasashen Japan da Norway da Ingila, wadanda mutanensu ne suka fi yawa a hannun yan tawaye suke korafin rashin samun wani labari na kirki a game da abin dake gudana a Aljeriya.

Nigerianische Truppen bereiten sich auf Einsatz in Mali vor
Sojojin Najeriya cikin rundunar ECOWAS a MaliHoto: Reuters

Jaridar Bild Zeitung tayi tambayar shin idan Faransa bata sami nasarar kwantar da rikicin yan tawaye a Mali ba, mayakan kungioyoiyin zasu mamaye nahiyar Afrika ne baki daya? Jaridar tace da farko yan tawayen sun mamaye kasar Mali, yanzu kuma ga Aljeriya. To daga nan kuma sai ina? Yankin arewacin Afirka da yankin Sahel yanzu haka dai suna cikin mummunan hadari na fadawa hannun yan tawaye musulmi dake iya zama barazana ba ma ga yankunan ko nahiyar Atfrika ba, amma har ga nahiyar Turai. Hakan ya sanya jaridar Die Welt ta kai ga tambayar: shin kuwa Faransa tana iya samun nasarar wannan yaki ita kadai? Ko da shike a lokacin wani taro na kungiyar hadin kan Turai a Bruessels bisa amsa rokon Faransa, kungiyar ta baiyana cikakken goyon bayanta ga matakan Paris, amma NATO ta sanar da cewar ba zata tura sojojinta zuwa rikicin na Mali ba, in banda taimakon a fannin jigilar sojoji, kayan magunguna da abubuwan da sojojin na Faransa suke bukata dokjin tafiyar da yakin a Mali.

A karshe jaridar Neue Zürcher Zeitung tace hare-hare jiragen saman yakin Faransa kan yantawayen da suka mamaye arewacin Mali, wani abu ne dabam mai sauki, idan aka kwatanta da aiyukan da mayakan kasa na Faransa suka sanya a gaba yanzu na kwato wannan yanki daga hannun yan tawayen. Wannan dai aiki ne mai sarkakiya, inji jaridar, saboda yan tawayen suna iya amfani da dabaru masu yawa, saboda su kadai ne suka san wannan yanki cikinsa da wajensa.

Francois Hollande tritt Nkosazana Dlamini-Zuma
Shugaban Faransa Francois Hollande da shugabar hukumar kungiyar AU Nkosazana Dlamini ZumaHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas