1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar wutar daji a Australiya

October 23, 2013

Wutar daji na ci gaba da yin barazana a sassa daban-daban na kasar Australiya, musamman ma a jihar New South Wales.

https://p.dw.com/p/1A54X
Hoto: picture-alliance/dpa

Jami'an kashe gobara a kasar Australiya na ci gaba da kokarin shawo kan matsalar zafi mai tsanani da busasshiyar iska a dai dai lokacin da wutar daji ke kara yaduwa a kasar, kimanin mako guda da bala'in ya afka musu wanda kuma a ke fargabar wutar za ta kara kazanta saboda tabarbarewar yanayi.

kawo yanzu dai an samu labarin yaduwar wutar dajin a gurare 71, inda rahotanni ke nuni da cewa jami'an kashe gobarar na ganin guda 29 daga ciki sun fi karfinsu a ke kokarin da suke ci gaba da yi na shawo kan wutar dajin data mamaye yankuna da dama a jihar New South Wales.

An dai sanya dokar ta baci a yankin, inda har ya zuwa yanzu ake ci gaba da yin gargadi ga al'ummar dake zaune a wannan yanki kan su zamo masu kula sosai, duk kuwa da cewa kawo yanzu babu wani rahoto dake nuni da kara samun asarar dukiyoyi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammed Nasiru Awal.