1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar yunwa a Duniya nan da 2021

December 6, 2012

Hukumar kula da abinci ta Duniya wato FAO, ta bayyana damuwa dangane da ƙalubalen da Duniya ke fuskanta dangane da karancin abinci a rahotanta na shekara.

https://p.dw.com/p/16x0n
Hoto: AP

Hukumar kula da cimaka ta Duniya da ke ƙarkashin Majalisar Ɗinkin Duniya, wato FAO, ta wallafa wani rahotonta a dangane da kalubalen da ke tattare da duniya a game da karanci abinci,inda rahoton ya nuna damuwarsa ga matsalar da kan iya shafuwar dubban milyoyin jama'a nan da shekara ta 2021.

A wani zaman taronta na shekara shekara da ta yi ne a cibiyarta da ke birnin Roma na ƙasar Italiya, hukumar ta wallafa rahoton a wannan Alhamis inda ta sake jaddadawa manyan kasashen duniya bukatar samo da hanyoyi domin fuskantar matsalar karancin abinci a duniya. Rahoton ya kara bayana cewar nan gaba sakamakon sauyin yanayi da duniya ke fama da shi, za a samu ragowar wadatacen abinci da kusan kaso 1 da digo 7 na jimlar cimakar da ake amfani da ita kowace shekara a Duniya. Duk da cewar,a wannan shekarar, an samu waddatatun ruwan sama a wasu yankunan duniya musamman ma inda ake yawan fuskantar matsalar karancin abinci,irin su latine Amurka, da kuma a yankunan kudu ga sahara na Afrika, to sai dai wata matsalar ta daban ita ce ambaliyar ruwan da ta kalubalanci yankunan inda kawo yanzu dubbun dubantan jama'a ne ke cikin bukatar abun sakawa a baki.

José Graziano da Silva, FAO
José Graziano da SilvaHoto: DW/R. Belincanta

Jamhuriyar Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fama da matsalar karancin abinci lokaci zuwa lokaci bugu da kari, ƙasar ta yi fama da ambaliyar ruwan sama a wannan shekarar. To ko me wannan sanarwar ta ke nufi ga ƙasashe 'yan rabbana ka wadata mu? Bangna Jibo, shugaban ƙungiyar manoman karkara ta kasa a Jamhuriyar Nijar da ma Afrika ta yamma, ya ce suna maraba da wannan batun domin zai faɗakar da magabata.

Ko baya ga wannan matsalar ta karancin ruwan sama da ma ambaliyar da ake fuskanta, hukumar ta ce kusan kashi 40 na guraren da ake noma ne ke tabarbarewa ta yadda albarkatun gonakai ke raguwa azahiri.

To saidai Bangna Jobo ya ce nan bada jimawa ba ma za su zauna su tautauna akan wannan rahoton da hukumar ta bayar domin bullo da wasu dabaru.

Welthungerhilfe Horn von Afrika Somalia
Hoto: AP

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da hukumar ta ƙasa da ƙasa ke jan kunnan magabatan ƙasashen Duniya gurin ɓullo da wasu dabaru domin fuskantar ƙalubalen karancin abinci. Bangna Jibo ya ce akwai yadda za a iya yi idan har a shurari shawarar da suke badawa.

Abun jira a gani shi ne na aiwatar da jerin shawarwarin a maimakon tarurukan zaman shan shayi,inda galibin takardun ke fadawa cikin kwadon mantuwa.

Mawallafi: Issufou Mamane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar