1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar yunwa a Sudan ta Kudu

March 14, 2014

Tun bayan da rikicin kabilanci ya barke a watan Disambar shekarar da ta gabata, kasar ke fama da matsalar karancin abinci.

https://p.dw.com/p/1BPbI
Hoto: Reuters

Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amirka sun yi gargadin cewa za'a fuskanci matsalar yunwa a kasar Sudan ta Kudu in har bangaren gwamnati da na 'yan tawayen kasar suka ci gaba da kin mutunta yarjejeniyar sulhu da suka cimma a tsakaninsu. A watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2013 ne dai fadan kabilancin ya barke tsakanin dakarun sojin kasar dake goyon bayan Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudn da kuma tsohon mataimakinsa da ya sauke daga kan karagar mulki Riek Machar, inda kuma tun daga nan ne kasar ke fama da matsalar karancin abinci. A hannu guda kuma a yayin taron da suka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha wato Ethiopia, shugabannin kasashen gabashin Afirka sun amince su tura dakarunsu zuwa Sudan ta Kudun a matsayin masu sanya idanu a yankin baki daya. Dubbban mutane ne dai suka rasa rayukansu yayin da wasu dubun- dubatar kumai suka rasa matsugunansu sakamakon wannan rikici da yake neman juyewa izuwa yakin basasa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar