1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barroso ya gabatar da manufofinsa ga majalisar Turai a birnin Brussels

Mohammad Nasiru AwalJanuary 27, 2005

Sabon shugaban hukumar zartaswar kungiyar EU Jose Manuel Barroso ya gabatar da jerin ayyukan da hukumarsa ta kuduri aniyar yi a cikin shekaru 5 masu zuwa.

https://p.dw.com/p/BvdQ
Jose Manuel Barroso a birnin Brussels
Jose Manuel Barroso a birnin BrusselsHoto: AP

Wadata, nuna zumunci da kuma tabbatar da tsaro na daga cikin manufofin sabon shugaban hukumar zartaswar KTT Jose Manuel Barroso. Shugaban na hukumar kungiyar EU ya bayyana haka ne a wani jawabi mai kama da gabatar da manufofin wata gwamnati da ya yiwa majalisar Turai dake birnin Brussels. Mista Barroso ya ce da shi da sauran kwamishinoninsa su 24 zasu fi mayar da hankali akan muhimman batutuwa amma ba kasancewa tamkar ´yan amshin shatan kasashen kungiyar EU ba. Mista Barroso ya ce bai kamata nahiyar Turai ta zama ´yar rakiya a harkokin tattalin arzikin duniya ba.

"Alhakin da ya rataya wuyanmu yanzu shine mu tsaya tsayin daka wajen aiwatar da sahihan canje-canje don kirkiro sabbin guraben aiki, musamman a wannan zamani na tserereniyar ciniki a duniya."

Kafin dai a yi haka dole ne a aiwatar da ka´i´dojin yarjejeniyar birnin Lissbon wadda kasashen kungiyar EU ke fatali da ita tun kimanin shekaru 5 da suka gabata. Kara zuba jari a harkar ba da ilimi da tsarin fansho mai nagarta da kuma kare muhalli na da muhimmanci wajen cimma manufar da aka sa gaba. Hakazalika wajibi ne a ci-gaba da tuntubar juna da kasashen gabashin Turai da na yankin GTT da kuma arewacin Afirka muddin a na son a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Turai baki daya.

"Babbar manufar mu dangane da ketare ita ce tattaunawar daukar kasar Turkiya cikin kungiyar EU da kuma tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasashe makwabta. Hakan kuwa yana da muhimmanci ga dorewar mulkin demukiradiya da tsaro a cikin Turai."

Dole ne kungiyar EU ta yi magana da murya daya a dangane da manufofinta na ketare da kuma kokarin da take yi na samun fada a ji a cikin MDD, inji mista Barroso. To sai dai Jamus wadda ke kokarin samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu tana adawa da bawa kungiyar EU wannan kujera. Mista Barroso yayi fatan samun goyon bayan majalisar a cecekucen da ake yi game da kasafin kudin hukumar sa, musamman a yanzu da wasu kasashen kungiyar ke son a rage yawan kudaden da ake warewa hukumar. Mista Barroso yayi korafin cewa karancin kudi ka iya dakushe ayyukan hukumarsa. Duk da wannan halin da ake ciki shugaban majalisar zartaswar kungiyar EU kuma FM Luxemburg Jean-Claude Junker da sauran ´yan majalisar Turai sun yabawa manufofin mista Barroso da cewa zasu taimaka wajen daga martabar nahiyar Turai.