1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun tsaro a jamhuriyar Afirka ta tsakiya

September 6, 2010

Hukumomin jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun kama wasu 'yan Slovakiya bisa zargin yunƙurin juyin mulki.

https://p.dw.com/p/P5Kt
Shugaba BozizeHoto: AP

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta kama wasu 'yan ƙasar Slovakia sama da goma bisa zargin yunƙurin juyin mulki ga shugaba Francois Bozize. Kakakin gwamnatin ƙasar wato Fidele Ngouandjika , yace hukumomin Bangui sun yi jigilar sojojin hayan na ƙasar waje i zuwa babban birni daga inda aka kamasu a Nola da ke yammacin ƙasar.

 Ita dai gwamantin ta jamhuriyar Afirka ta tsakiya ta ce ta yi nasarar daƙile wani yunƙurin juyin mulki da aka so shirya mata daga waje, tare da kame kusan mutane 12 'yan kasar Slovakia, da suka shiga Jamhuriyar Afirtka ta Tsakiyan ba tare da izini ba. Rahotannin sun bayyana cewa tun ranar jumma'ar data gabata ne, jami'an tsaro suka kama yan ƙasar ta Slovakia, a lokacin da suke koƙarin taryar wani jirgi mai ɗauke da muggan makamai a wani gari da ke da tazarar kilometa 600 da yammacin babban birnin ƙasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala