Batun tsaro na barazana ga hadin kan Najeriya
October 29, 2012A shekarun baya dai ba a san hare-hare na ta'adanci da kunar bakin wake ba a Najeriya. Amma a yanzu suna ci gaba da zama ruwan dare duk da matakan tsaro da gwamnati ta dade tana ikirarin dauka a kansu. Tuni dai Kokarin tabbatar da tsaron ya haifar da tsoro a zukattun 'yan Najeriyar da ke cike da fargabar wannan matsala.
Salon irin na dauki dai dai da ake yi wa jama'a da kuma jami'an tsaron kasar na kara zama babbar barazana ga harkokin tsaro. Masharhanta sun bayyana ta da wacce kasar bata taba fuskantar irinta ba tun bayan samun 'yancin kai shekaru 52 da suka gabata, duk kuwa da fafata yaki da ta yi a 1967 zuwa 1970. Major Yahya Shunku mai ritaya kwararre ne a harkar tsaron Najeriyar ya ce‘ " Alhakin yan sandan ciki ne su tabbatar da cewa duk wani abu da zai ta da hankalin kasa sun shawo kansa kaman irin tashin bama-baman nan. To amma daga lokacin da aka fara samun tashin bama –baman nan babu wani darakta na hukumar SSS na wata jiha da aka kama da sakaci a aikinsa, duk wanda ake kamawa sai dai ka ji an ce 'yan sanda."
Wadanda ke da alhakin tabbatar da tsaro a Najeriya
Irin kwan gaba kwan bayan da wannan matsala ta ta'adanci ke ci gaba da yi a Najeriya ya sa ta zama kadangaren bakin tulu. Sai dai makudan kudin da aka kasaftawa sashin tsaro da bana suka zartar Naira triliyan guda. Lamarin ya sanya nuna damuwa bisa ga barazanar da matsalar ta'adanci ke yi ga hadin kan Najeriyar da a yanzu ke fuskantar sabon kalubale na bangaranci. Abinda ya sanya Dr Abubakar Umar Kari masanin hallayar jama'a da ke jami'ar Abuja bayyana tsoron cewa " Abubuwa sun tabarbare matuka da ke nuna komai na iya faruwa, tun da abubuwan da ke faruwa a yanzu wadanda sabbi ne ba a Arewa ba a ma Najeriya baki daya. Sai dai kawai a zo ayi ta Magana ta fatar baki ana cewa yau za'a dau wannan mataki, gobe a yi ikirarin wancan, amma babu matakin da ake dauka, a yanzu dai babu ban san ko a nana gaba ba.''
Mafita ga matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya
Tuni wasu ke hangen wauta ce a tekun maganinki Allah ya sanya ci gaba da laluben mafita. Kwararru sun dade da nanata bukatar sulhu. Amma ga Malam Bashir Baba da ke zama mai sharhi a kan al'ammuran hanya daya ce ta sauki. "Ana iya samun sauki idan mahukunta wadanda amanar jama'a take hannunsu suka fitar da son zuciya. To ana iya samun sauki amma daina wannan al'ammari gaskiya ni ba ganshi ba."
Anobar da wannan matsala ta rashin tsaro da Najeriya ke fiskanta, na zama abu mai ta da hankali ga makomar kasar da a lokutan baya ke zama abin misalai wajen zaman lafiya da kwanciya hankali.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal