1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Bayajidda: Gwarzon kasar Hausa

Ahmed Salisu LMJ
January 10, 2018

Masana tarihi na tababa game da gaskiyar tarihin Bayajidda amma mutumin wanda ake dauka a matsayin gwarzo na ci gaba da kasancewa a tarihin Malam Bahaushe.

https://p.dw.com/p/2qe5L
DW African Roots- Bayajidda
Bayajidda da amariyarsa Sarauniyar DauraHoto: Comic Republic

Rayuwarsa: 

Babu wani kwakkwaran bayani da ake da shi game da shekarar da aka haifi Bayajidda da ma sanda ya rasu kasancewar galibin tarihinsa da aka bayar, ta fatar baka ne. Ana tunanin cewar asalinsa mutumin Bagadaza ne a kasar Iraki kuma bayan zuwansa daular Borno ne ya koma Daura da ke jihar Katsina da zama.

 

Asalin tarihinsa: 

Wasu na cewar Bayajidda ya bayyana ne tsakanin karni na 16 zuwa na 19 amma kuma akwai shaidar kasancewarsa a al'adar Hausawa tun cikin karni na 9 zuwa na 10.

 

Suna: 

Ana zaton asalin sunansa Abu Zaid. An samo sunansa na Hausa da aka sanya masa wato Bayajidda daga jimlar nan ta "Ba ya ji da”, ma'ana a baya ba ya jin Hausa.

Tarihin Bayajidda da asalin Hausa bakwai a Najeriya

Macijiya: 

An bayyana cewar Bayajidda ne ya kashe wata macijiya a rijiyar nan ta Kusugu da ke Daura. Macijiyar a wancan lokacin ta addabi mutanen garin inda take hana su dibar ruwa. Sukan samu dama ta jan ruwa ne sau daya a mako wato ranar Jumma'a. Duk da gargadin da aka yi masa, Bayajidda ya yi kokarin dibar ruwa a ranar Alhamis amma ya gamu da fushin macijiya sai dai ya samu nasarar fille mata kai da takobinsa.

 

Aure: 

Sarauniya Daurama ta yi alkawarin ba da rabin kasarta ga duk wanda ya kashe macijiyar da ke rijiyar Kusugu, amma Bayajidda bai karba ba maimakon haka sai ya bukaci ya auri sarauniyar, wanda a baya ba a taba ji ba kasancewar matan da ke mulki a wancan lokacin ba sa yin aure. To amma duk da haka Daurama ta auri Bayajidda saboda irin abin da ya yi wa jama'ar Daura.

 

Nasarori: 

Tarihi na daukar Bayajidda a matsayin wanda ya sauya lamura a masarautar Daura, domin kuwa kafin zuwansa mata ne kawai ke mulki. Wannan lamari ya sauya bayan da Daurama ta aure shi kuma daga bisani 'ya'yan da suka haifa suka gaje ta.

 

Garuruwan kasar Hausa: 

Bayajidda ya haifi 'ya'ya uku, na farko shi ne Biram wanda ya haifa da 'yar sarkin daular Borno, sai kuma Bawo wanda ya haifa da Sarauniya Daurama na ukun kuma ya haife shi ne da wata kwarkwara. Bawo ya haifi 'ya'ya shidda kuma tare da kawunsu wato Biram sune suka mulki garuruwan da ake kira Hausa bakwai wanda suka hada da Daura da Kano da Katsina da Zariya da Gobir. Sauran sun hada da Rano da kuma Hadeja.

 

Karkashin shiri na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.