1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilan da suka sa APC ta lashe zabe a Bayelsa

Muhammad Bello AMA
November 18, 2019

Hukumar zabe mai zamankanta INEC a Bayelsa ta bayyana dan takarar gwamna na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya doke abokin hamayyarsa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

https://p.dw.com/p/3TEdZ
Nigeria Symbolbild Wahl
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Bangarori da dama na mamakin yadda gaggan 'yan siyasar jihar Bayelsa kusoshi a jam'iyyar adawa ta PDP ciki har da tsohon shugaban tarayyar Najeriya Dakta GoodLuck Jonathan suka zuba ido jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta kwace kujerar gwamnan jihar.

Bayannai sun tabbatar da cewar wanyan 'yan siyasa ba su gamsu da yadda gwamnan jihar mai barin gado Serieke Dicksen ya ringa tafiyar da alammuran jihar shi kadai abinsa ba a cikin yanyi da wasu ke ganin na kama karya ne, kana kuma hatta fitar da dan takarar jam'iyyar gwamna Dicksen ne kadai ya yi a gabansa. Masu sharhi nna ganin faduwar zaben gwamnan na da nasaba da yadda Uwar gidan tsohon shugaban kasar Madam Patience Jonathan ta taka rawa sosai a siyasar jihar inda ta bayyana dan takarar jamiyyar APC  da cewar dan ta ne, lamarin da ya haddasa juyin juya hali na siyasa, da samun kwanciyar hankali biyo bayan sanar da sakamakon zaben na gwamna.

Sakamakon zaben ya samu karbuwa daga wasu 'yan jihar Mr Emmanuel Ibe daya ne daga cikin wadanda suka yi zabe ya ce "ya yi amannar cewar sabuwar gwamnatin da za ta kama mulki a jihar za ta yi iya kokarin ta wajen tabbatar da ci gaban jihar Bayelsa." Haka dai bangarorin 'yan jihar da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan yadda aka gudanar da zaben da kuma sakamkon da suka gani wanda galibi suka nuna gamsuwa da shi.