1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bayelsa: Hukuncin kotu ya bar baya da kura

Muhammad Bello
August 18, 2020

Tun bayan hukuncin wata kotu a Najeriya da ta ce gwamnan jihar Bayelsa ya sauka a sake wani sabon zabe, lamarin ya janyo cece-kuce bayan da hukumar zabe ta kasa ta fidda sanarwa kan hukuncin.

https://p.dw.com/p/3h9GR
Nigeria Homosexualität Polizei-Razzia in Lagos
Hoto: Reuters/T. Adelaja

Hukuncin kotun na sauke gwamnan jihar ta Bayelsa Mr Douye Dire tare da bukatar a sake sabon zabe, ya zo wa mutane dama da mamaki a ciki da wajen jihar.

Akwai dai kararraki da dama da ‘yan jamiyyu kusan uku suka shigar a gaban kotuna daban daban, sai dai bayan korar wasu daga cikin kararrakin kan zaben na Bayelsa, karar da a yanzu ta yi tasiri, ita ce ta kokawar da jamiyyar Advance Nigeria Democratic Party ta yi, cewar hukumar zabe ba ta sanya sunanta a jerin jamiyyu da suka tsaya zaben ba, dan haka kotun ta Abuja ta yi amfani da wannan hujja ta sauke gwamnan daga kan mulki.

Sai dai kuma, hukumar zabe ta kasa ta fidda bayanai cewar, dama jamiyyar ta ANDP, ba ta cikin zaben saboda rashin cika kaidoji.

Barr Higher King, wani lauya ne mai zaman kansa.

Ya ce “ya kamata ko wane bangare ya bi umarnin hukuncin kotu har sai an kai ga daukaka kara, sannan a saurari abin da zai biyo baya. Ko da yake dai batutuwa masu sarkakkiya da dama sun bujiro game da hukuncin, amma dai abi umarnin kotu, kuma ‘yan jamiyyun da ke cikin takara su ci gaba da shirin sake zabe, har sai idan an samu sabanin hukunci daga kotun koli“.

Tun bayan yanke wannan hukunci dai, jama’ar jihar suna ta bayyana ra’ayoyin mabanbanta, yayin da wasu ke murna, wasu kuwa na kokawa