1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Leverkusen ta ba wa Bayern kashi

Mouhamadou Awal Balarabe YB
February 4, 2019

Yayin da a gasar Bundesliga a Jamus Bayer Leverkusen ta ba wa Bayern Munich kashi an samu baraka a kwamitin zartaswa na CAF dangane da gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka a shekara ta 2021.

https://p.dw.com/p/3CgSQ
Deutschland Bundesliga Bayer Leverkusen - Bayern München | Leon Bailey
Hoto: imago/H. Bucco

Wata baraka ta kunno kai a kwamitin zartaswa na CAF dangane da gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afirka na shekara ta 2021, inda daya daga cikin mambobi Musa Bility dan kasar Laberiya ya zargi shugaban hukumar Ahmad Ahmad da keta ka'ida wajen danka bakuncin gasar 2021 ga Kamaru ba tare da shawartarsu ba. Shi dai Bility ya ce shugaban hukumar kwallon kafar ta kasashen Afirka ya yi gaban kansa wajen daukar wannan mataki, lamarin da ke karan tsaye ga dokokin kwallon Afirka, kuma ke sake farfado da munanan dabi'u da tsohon shugaban CAF ya yi kaurin suna a kai. Saboda haka ne Musa Bility ya yi murabus daga mukamansa biyu da yake rike da su a hukumar kwallon kafar Afirka, kamar daga na shugabancin kwamitin shirya gasar kwallon kafar ta kasashen Afirka zuwa ga mamba na kwamitin gaggawa na wannan hukuma.
Shi dai Musa Bility da ya taba shugabantar hukumar kwallon kafa ta Laberiya ya saba takun saka da shugabannin CAF, inda ko a shekara ta 2012 ya kai Issa Hayatou kara kotu bayan da ya kwaskware kundin tsarin hukumar kwallon kafa da aka yi domin haramta wa Jacques Anouma na Cote d'Ivoire  damar tsayawa takarar shugabancin hukumar, ko da shi ke bai samu nasara ba.
A Jamhuriyar Nijar kuwa, Matsalar wutar lantarki ta sa an dage wasu daga cikin wasannin neman lashe kofin kwallon kafa na kasashen Afirka na 'yan kasa da shekaru 20 da ke gudana a Maradi, lamarin da ke jefa shakku kan shirin da kasar ta ce ta yi dangane da gasar kasa da kasa ta kwallon kafa da wannan ke kasancewa na biyu da take daukar bakuncinsa a Afirka.
A gasar kalubale na Confederations Cup kuwa, CS Sfaxien ta Tunisiya ta samu nasara a kan 'yar uwarta Etoile du Sahel ita ma daga Tunisiya. Yayin da Raja Casablanca ta Moroko ta tashi kunnen doki 1-1 da Hassania Agadir. Irin wannan sakamakon na daya ko ta ina aka samu tsakanin AS Otôho ta Kwango da RS Berkane ta Maroko.

Musa Bility
Musa Bility ya kasance sha gwagwarmaya a fagen wasannin na AfirkaHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

A fagen Bundesliga, an gudanar da wasannin mako na 20 a ranakun Juma'a da Asabar da Lahadi, kuma babban abin ta'ajibi shi ne kashi da Bayern Munich da ke rike da kambun zakaran Jamus ta sha a hannun Bayer Leverkusen da (3-1). Hasali ma Leon Goretzka na Bayern ne ya fara zura kwallo a ragar masu masaukin baki minti 41 da fara wasa.

Amma bayan dawowa hutun rabin lokaci, 'yan wasan Bayer Leverkusen sun farfado tare da barza wa Munich aya a hannu, inda  Leon Bailey da Kevin Volland da Lucas Alario suka zura kwallaye uku. Wannan kaye da ke zama irinsa na hudu tun bayan fara kakar 2018-2019.
A fagen Tennis, Jamus ta cancanci shiga sabon zubin gasar kasa da kasa ta Davis Cup da za ta gudana a watan Nuwamba mai zuwa bayan da ta doke Hangari. Amma dan wasan Tennis da ya fi tashe a Jamus Alexander Zverev, wanda shi ne mai matsayi na uku a teburin Tennis a duniya, ya tabbatar da cewa ba zai shiga a dama da shi ba, saboda sabon fasalin bai kwanta masa ba.
Sabon tsarin Davis, wanda aka shirya bisa shawarwarin tauraron Tennis na kasar Spain da kuma dan wasan kwallon Tennis Gerard Piqué na Faransa, ya tanadi wasanni uku a maimakon biyar idan aka shiga matakai na kurkusa da na karshe, kuma  sun gudana a wuri daya a cikin mako guda.

Tennis Zverev - Chardy Melbourne Australian Open
Alexander Zverev fitaccen dan wasan Tennis a JamusHoto: Reuters/E. Su