1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bemba ya yi watsi da sakamakon zaɓen ƙasar Kwango.

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubj

Ɗan takara a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, Jean-Pierre Bemba, wanda ya sha kaye a zaɓen, ya yi watsi da sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta, ta bayar jiya, inda ta ce shugaba mai ci yanzu Joseph Kabila ne ya lashe zaɓen.

Da yake jawabi a kan wata tasahar talabijin mai zaman kanta da yake mallaka, Jean-Pierre Bemba, tsohon shugaban ’yan tawaye, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin riƙon ƙwaryar da ta yi mulki a ƙasar kafin zaɓen ya bayyana cewa, yana nadamar sanar da jama’an ƙasar da kuma al’umman gamayyar ƙasa da ƙasa, ƙin amincewarsa da sakamakon zaɓen, saboda a nasa ganin, bai dace da ainihin ƙuri’un da aka ka da ba.

Bemba dai ya ce zai yi amfani ne da duk hanyoyin shari’a wajen ƙalubalantar sakamakon.