1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bene: Majalisar dokoki ta yi watsi da gyaran kundin mulki

Abdourahamane Hassane
April 5, 2017

Majalisar dokokin Jamhuriyar Bene ta yi watsi da kudirin da shugaban kasar Patrice Talon ya gabatar na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/2ahrl
Benin Präsidentschaftskandidat  Abdoulaye Bio Tchane
Hoto: picture-alliance/AA

Kudirin shugaban wanda ke neman a kayade wa'adin mulki daya kawai kacal na shekaru shidda ga kowane shugaban da zai hau mulki a kasar, yawancin 'yan majalisun dokokin kasar sun hau kujerar naki a kansa. Sai dai kuma manazarta al'amuran yau da gobe na cewar shugaban kasar na iya shirya kuri'ar jin ra'ayin al'umma a game da wannan batu wanda bisa ga dukkan alamu ya nace sai an yi wadannan sauye-sauye.