1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benedikt na 16 zai ajiye aikin Paparoma

February 11, 2013

Dalili da ciwon tsufa,Paparoma Benedikt na 16 zai sauka daga kujerar shugaban ɗarikar Roman Katolika ta duniya a ranar 28 ga watan Fabrairun 2013.

https://p.dw.com/p/17c1E
Hoto: Getty Images

Paparoma Benedikt na 16 zai yi murabus daga mukaminsa na shugaban darikar Roman katolika ta duniya sakamakon tsufa da ya ke fama da ita a halin yanzu. Fadarsa da ke birnin Roma na Italiya da ta bayar da wannan labarin ta ce ranar 28 ga wannan wata na fabreru, wata nan da kwanaki 17 masu zuwa ne, paparoman da kansa zai aiwatar da wannan mataki.

Cikin wani sako da aka fassara cikin harsuna daban daban na duniya, Benedikt na 16 ya nunar da cewa ba shi da karfin da zai ci gaba da shugabantar darikar katolika ta duniya yadda ya kamata.

Shi dai Benedikt na 16 wanda zai cika shekaru 86 nan da watannin biyu masu zuwa ya dare kan wannan kujerar mai alfarma ne shekaru takwas da suka gabata. Shi ne shugaban darikar Katolika na 265 tun bayan kafata a karnin 11, kana bajamushe na farko da ya zama Paparoma.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas