1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bengarorin kasar Libiya za su tattauna a cikin kasar

Salissou BoukariFebruary 11, 2015

A wannan Laraba ce (11.02.2015) za'a soma wani taron share fage tsakanin bengarorin kasar Libiya masu gaba da juna a garin Ghadames da ke Kudu maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/1EZZw
Hoto: Reuters/P. Albouy

Wannan tattaunawa na wakana ne a karklashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya a cewar wata majiya mai tushe ta ma'aikatan Majalisar da ke kasar ta Libiya. Bengarorin dai sun hada da 'yan majalisun dokokin kasar da kasashen duniya suka aminta da su, da kuma 'yan majalisar ta farko da aka rushe amma kuma suke ci gaba da nasu aiki a birnin Tripoli. Rahotanni sun ce an ga shugaban ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya Bernardino Leon ya isa wannan birni da ke a nisan kilo-mita 600 a kudu maso yammacin kasar inda za a yi wannan tattaunawa.

A wata sanarwa da ta fitar a baya, tawagar Majalisar Dinkin Duniyar a kasar Libiya, ta yi batun cewa za a gudanar da wani zaman taron share fagen da zai gudana a kasar ta Libiya, amma kuma babu wani cikeken bayani na lokacin. Kasar ta Libiya ta shiga cikin wani mawuyacin hali tun bayan rushewar gwamnatin Marigayi Muammar Gaddafi a watan Octoba na 2011.