1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Benuwe: PDP ta lashe zaben gwamna

Ramatu Garba Baba
March 24, 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta a jahar ta Benuwe ce ta sanar da Mista Samuel Ortom na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamna da aka sake gudanarwa a wasu hukumomin jahar 22 a jiya Asabar.

https://p.dw.com/p/3Fb4X
Wahlen Nigeria Wahlausgang
Hoto: AP

Sakamakon zaben gwamnan jihar ta Binuwe,  ya nuna yadda Ortom ya lashe zaben da kuri'u 434, 473 inda ya doke abokin takararsa na jama'iyyar APC, Mista Emmanuel Jime wanda ya sami kuri'u 345, 155.

A jiya Asabar ne dai aka kammala zaben jihar bayan da aka gudanar da zaben da ba'a kamalla shi ba a wasu yankunan kananan hukumomin jihar 22.