1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin 'yancin aikin jarida a Nijar

Gazali Abdou Tassawa/Ahmed SalisuNovember 30, 2014

Ana cigaba da bikin raya ranar 'yancin aikin jarida a Jamhuriyar Nijar wanda shugaban kasar Alhaji Mahammadu Isuhu ya kaddamar shekaru ukun da suka gabata.

https://p.dw.com/p/1DxIi
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Ware wannan rana ya biyo bayan wata matsaya da kasashen Afirka suka cimma da ta tanadi haramta daure manema labarai bisa kuskuran alkalami lokacin da ya ke aikinsa.

Nijar dai ita ce kasa ta farko da fara gudanar da wannan biki da ya samu halartar kafofin watsa labarai na ciki da wajen kasar kuma gwamnatin kasar ta ce ta yi hakan ne don mutunta 'yancin fadin albarkacin baki da kuma inganta tsarin dimokradiyya kamar yadda Yahouza Sadissou Madobi ministan sadarwa na Nijar din ya shaida.

To sai dai a hannu guda Malam Abubakar Diallo shugaban dakin shawarar na 'yan jarida na Nijar din na ganin da akwai sauran aiki a gaban magabata da su kansu 'yan jarida.