1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Kashe kudi fiye da kima a bukukuwan aure

Julia Jaki RGB/MNA
January 14, 2020

Bukukuwan aure da ake kashe makudan kudade ya zama ruwan dare a tsakanin angwaye da amare na kasashen Afirka, duk da talauci da matsin tattalin arziki da ya adabi al'umma a nahiyar.

https://p.dw.com/p/3WB6H
Kenia Hochzeit
Hoto: Getty Images/AFP/F. Lerneryd

Bukukuwan aure da ake kashe makudan kudade za a iya cewa yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin angwaye da amare na kasashen Afirka, duk kuwa da talauci da matsin tattalin arziki da ya adabi al'umma a nahiyar. Akasarin bukukuwan da ake gudanarwa na lakume dubban daloli, kamar yadda bincike ya gano.

Ga akasarin masoya da ke da shirin aure a Afrika, burinsu su yi biki na kece raini. Wasu na son yin irin bikin da za a dade ana dambarwa a kai, a yayin da ake son amfani da taron bikin don nuna irin son da suke yi wa juna. Ana dai gayyatar daruruwan jama'a don hallatar bikin aure.

Arnold da Susan 'yan kasar Afrika ta Kudu na daga cikin wadanda suka gudanar da kasaitaccen biki watanni biyu da suka gabata. Mutum kimanin 700 suka hallaci bikin, a cewar amaryar, Susan Godo-Kaziboni, mafarkin da ta dade tana yi ne ya tabbata.

''Tun ina yarinya nake mafarkin na yi bikin kece raini, ba wai kawai bikin da za a yi a tsakanin 'yan uwa da dangi ba. Shi yasa na yi ta rokon Allah ya hada ni da wanda ra'ayinmu zai zo daya, kuma hakan aka yi, an yi bikin yadda raina ya so.''

Susan Godo-Kaziboni da angonta Arnold Kaziboni
Susan Godo-Kaziboni da angonta Arnold KaziboniHoto: Julia Jaki

Susan da Arnold sun kashe akalla dala dubu biyar da dari biyar a sha'anin bikin, ninkin ba ninkin albashinsu na wata akalla hudu. Sai dai sun kwashi akalla shekaru uku suna shiri kamar yanda angon, Arnold Kaziboni, ya sheda.

''Mun soma shirin da wuri inda muka rage yawan kudin da muke kashewa a duk wata. Baya ga haka akwai wadanda suka taimaka mana, saboda haka da bikin ya zo ma, ba mu ji jiki ba, mun ji dadi muna kuma cike da godiya.''

Ra'ayi dai riga, wadannan sabbin ma'auratan na gaba, gudanar da kasaitatccen biki jidali ne da kuma azawa kai nauyi na ba gaira ba dalili. Shi ya sa suka zabi su dadada wa kansu maimakon kashe kudin da daga baya ka iya jefasu cikin kangin bashi, a cewar amaryar, Honey Mantyi-Vakala.

'Bamu da halin da za mu yi facaka kamar yadda yanzu ake yi a bukukuwan kasar nan. Bayan mun yi shawara, sai muka ga babu dalilin mu kashe kudi wajen gayyato tarin jama'a, maimakon hakan mun yi bikin a tsakanin dangi kawai, in ya so mu tafi hutun angwanci, daga ni sai mijina tun da muke son juna tsakaninmu ne bai shafi rayuwar sauran al'ummar yankinmu ba.''

Yin kasaitaccen bikin aure ba bakon abu ba ne kamar nan a kasar Yuganda
Yin kasaitaccen bikin aure ba bakon abu ba ne kamar nan a kasar Yuganda Hoto: DW/E. Lubega

Honey da minjinta Wongalethu dai sun kashe dala dari hudu kacal a bikinsu, sun yi amfani da sauran kudin da suka tara a sayan mota, suka kuma sami kudin zuwa hutun angwanci a kasar Thailand. To ka ya 'yan uwa da dangi suka ji da wannan matakin nasu? Ga abin da ango Wongalethu Vakala ke cewa:

"Mahaifiyata ce ke da burin yin kasaitaccen biki ganin ni ne dan fari, ta kashe kudi a tsara bikin. Amma ko da ta fada min, na ce mata ba na wannan ra'ayin. Da dama a cikin dangi ba su ji dadi ba, amma ni kuma ba zan sauya ra'ayina don su ba. Na sha suka amma daga baya ba yadda za su yi da ni haka suka hakura da ni.''

Wadannan ma'auratan dai sun shawarci jama'a da su kula, su yi amfani da dan gatarin nan naka da ya fi sari ka ba ni, don bayan bikin kowa zai watse a barku daga ku sai halinku da kuma abin da ya biyo baya wato bashi muddin aka guntsa fiye da karfin baki.