1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken makamai masu guba a Siriya

July 24, 2013

Wata tawaga ta wasu ƙwararru na Majalisar Ɗinkin Duniya ta isa a birnin Damascus na Siriya domin yin bincike a kan zargin yin amfanin da makamai masu guba.

https://p.dw.com/p/19Dqr
KOMBO - ARCHIV - Die deutsche UN-Abrüstungsbeauftragte Angela Kane, aufgenommen am 29.04.2008 in Paris und ein undatiertes Bild des schwedischen Giftgasexperte Åke Sellström. Kane und Sellström sind am 23.07.2013 auf ihrem Weg nach Syrien in Beirut eingetroffen. Sie wollen am 24.07.2013 nach Damaskus weiterreisen, berichteten Medien in Beirut. Dort sind mit der syrischen Führung Vorgespräche über die Arbeit einer UN-Expertengruppe für Chemiewaffen geplant. Das Team soll die Vorwürfe des Einsatzes von Chemiewaffen in Syrien prüfen. Fotos: epa/Scanpix (zu dpa:"UN-Chemiewaffenexperten auf dem Weg nach Syrien" vom 23.07.2013)
Hoto: picture-alliance/dpa

Angela Kane babbar jami'ar MDD da ke lura da shirin kwance ɗamarar yaƙi, da kuma Ake Sellstron shugaban hukumar binciken makamai masu guba na Majalisar ta Ɗinkin Duniya.

Za su tattauna da shugabannin Siriya domin samun izinin kai ziyara don yin bincike a cibiyoyin da ake zargin an yi amfani da makaman.Gwamnatin ta Siriya ita ce ta buƙaci Majalisar ta Ɗinkin Duniya da ta tura wakilanta don yin bincike.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu