1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar rufe majalisar dokokin Birtaniya na wucin gadi

Mohammad Nasiru Awal LMJ
August 28, 2019

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya nemi da a dakatar da ayyukan majalisar dokokin kasar tsawon wata guda.

https://p.dw.com/p/3OdUa
Frankreich G7 Gipfel in Biarritz | Boris Johnson
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kapeller

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya mika wa Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu bukatar a dakatar da aikin majalisar dokokin kasar daga tsakiyar watan Satumba zuwa tsakiyar watan Oktoba. A tsukin wannan lokaci ba za a shirya wani zama a majalisar ba.

Masu adawa da ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai EU ba tare da yarjejeniya ba, sun takaita lokacin, a wani mataki na amfani da doka don hana Birtaniyar ficewa daga EU a ranar 31 ga watan Oktoba ba da yarjejeniya ba. Sai dai Firaminista Johnson ya yi watsi da zargin da aka yi cewa yana son yi wa majalisar dan-waken zagaye ne a takaddamar da ake yi game da shirin ficewar.

Kakakin majalisar dokokin Birtaniya, John Bercow ya bayyana matakin na Firaminista Johnson da cewa ya karya dokar tsarin mulkin kasar.

A nata bangaren Hukumar Tarayyar Turai a ta bakin mai magana da yawunta, Mina Andreeva ta ce ba za ta tsoma baki a cikin batun ba. Ta ce EU ba ta tsokaci kan batutuwan siyasa na cikin gida na kasashe membobinta.