1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: May ta samu izinin kafa sabuwar gwamnati

Gazali Abdou Tasawa
June 9, 2017

Firaministar Birtaniya Theresa May ta sanar da shirin kafa sabuwar gwamnati bayan da ta dawo daga fadar Buckingham inda ta nemo izini daga sarauniya Elizabeth kamar yadda dokokin Birtaniyar suka tanada. 

https://p.dw.com/p/2ePvD
II. London Theresa May und Ehemann
Hoto: Reuters/T. Melville

A wani takaitaccen jawabi da ta gabatar bayan dawarta daga fadar ta Buckingham, Firaminista May wacce ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi mata na ta yi murabus bayan da jam'iyyarta ta samu koma-baya a zaben majalisar dokokin na ranar Alhamis, ta sha alwashin kafa gwamnati mai adalci da za ta tattauna batun ficewar kasar daga cikin kungiyar EU inda ta yi karin bayani tana mai cewa:

"Gwamnatin da zan kafa za ta kasance mai adalci a duk cikin abin da za ta yi ta yadda a tare za mu mutunta alkawarin da muka dauka na aiwatar da shirin ficewar Birtaniyar daga cikin kungiyar EU a tattaunawar da za mu soma nan da kwanaki 10."

Kafofin yada labaran Birtaniyar sun ruwaito cewa firaministar za ta yi kokarin kafa takaitacciyar gwamnati ta hanyar hada kai da jam'iyyar DUP ta Ireland ta Arewa mai kujeru 10 a majalisar dokoki.

Firaminista May ta shirya wannan zabe ne ainahi da nufin kara girman rinjayen da ke gare ta a majalisa, ta yadda za ta fi tunkarar tattaunawar ficewar kasar tata daga cikin EU a cikin kwarin gwiwa. Sai dai kuma ta wayi gari da baras da kujeru 12 a kan wadanda take da kafin zaben. Abin da ya rage mata kuzari a tattaunawar da za ta yi kan wannan batu da kasashen EU 27.